Ba mu yarda da ci gaban shugabanci mara kan gado ba – PDP

Daga AISHA ASAS

Babbar jam’iyyar bamayya a Nijeriya, PDP, ta ce duk da dai tana yi wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari barka da dawowa daga jinyar da ya je a Turai, amma ba ta yi na’am da zancen shugaban ba na cewa ‘yan Nijeriya su sa ran ganin “Ci gaba.”

A bayanin da ta fitar, PDP ta ce tana ra’ayin ko ma dai da wata manufa shugaban ya furta kalmar ‘Ci gaba’ ɗin, kada hakan ya yi nasaba da barin mulkinsa ya zuwa 29, Mayu, 2023.

Ta ci gaba da cewa hasali ma ‘yan Nijeriya ba su yarda da duk wani ci gaban da ke tattare da gazawar tattalin arziki da yunwa da fashi da sace-sacen mutane, take haƙƙoƙin jama’a da sauran su waɗanda suka tattaru suka mamaye gwamnatin APC ƙarƙashin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.

Haka nan ta ce, yayin da take sane da irin halin da ‘yan ƙasa ke ciki, tana mai bada shawarar wajibi ne waɗanda ke da hurumin jujjuya lamurran ƙasa su kwatanta adalci kada su ɗauki dala ba gammo.

PDP ta buƙaci Shugaba Buhari ya hanzarta yi wa ‘yan ƙasa bayani a kan yadda gwamnatinsa ta shirya biyan basussukan da ta kinkimo daga ƙetare a tsakanin watanni shidan da suka gabata wanda a cewarta tamkar jinginar da makomar ƙasar nan ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *