Katsina: Za a tura karnuka don su bada tsaro a makarantu

Daga FATUHU MUSTAPHA

A matsayin wani mataki na ƙokarin daƙile matsalar tsaro musamman ma a makarantun kwana, gwamnatin Jihar Katina ta amince da batun tura karnuka na musamman ya zuwa makarantun kwana domin su yi aiki tare da jami’an tsaro wajen bai wa makarantun kariya.

Tun farko, sai da gwamnatin jihar ta ɗauki matakin tura jami’an tsaro biyar-biyar zuwa makarantun kwana tare da ɗaga katangar kariya domin samar da tsaro a makarantun da lamarin ya shafa a jihar.

Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dr Badamasi Charanchi, ya bayyana wa manema labarai cewa gwamnati ta ɗauki matakin yin amfani da karnukan ne domin ƙarfafa wa jami’an tsaron da aka tura zuwa duka makarantun kwnanan jihar.

Ya ce, “An shawarce mu ne a kan mu yi amfani da karnuka wajen bada tsaro ga makaratun saboda karnukan na da basirar saurin gano duk wata matsalar tsaro da ke shirin aukuwa.

“Bayan tura su, karnukan za su riƙa taimakawa wajen farkar da ɗalibai da sauran jami’an tsaro dangane da wata matsala da ta shafi tsaro.

”Shawara ce da jami’an tsaro suka ba mu wanda muka ga akwai buƙatar ɗabaƙa ta duba da halin matsalar tsaron da ake fama da ita a yanzu. Kai ko a ofishin ‘yan sanda da gidajen attajirai ana amfani da karnuka don su yi aiki tare da jami’an tsaro da ƙungiyoyin ‘yan bijilanti.”

Gwamnan Jihar Katsina, Bello Masari, ya ce sai da suka farfaɗo da tsarin tsaro mai inganci a makarantun kafin aka sake buɗe su.

Jihar Katsina dai na daga cikin wuraren da ‘yan bindiga suka fi addaba da kashe-kashe da sace-sacen mutane a wannan ƙasa.