Boko Haram: Ministan Tsaro ya yi wa Jihar Borno tsinke

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Borno

A ci gaba da kai ziyarar ƙarfafa gwiwa ga sojojin da ke aikin samar da tsaro a jihar Borno, Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (ritaya), tare da Shugabanin Rundunonin Sojojin Nijeriya, sun yi wa birnin Maiduguri tsinke domin duba halin da ake ciki a yankin, a ranar Lahadi.

Kwamandan shalkwatar Rundunar Lafiya Dole da ke Maiduguri, Manjo Janar Farouq Yahaya, shi ne ya yi wa tawagar ministan marhabin, tare da yaba wa ƙoƙarin ministan da shugabanin sojojin dangane da ingantattun matakan da ministan tsaro tare da takwarorinsa ke ɗauka wajen ƙarfafa gwiwar rundunonin da ke aikin samar da tsaro a yankin.

Kazalika, ya ce dakarun sojojin da ke aikin samar da tsaro a yankin suna alfahari, farin-ciki da ziyarar ministan kana da damar tattauna matsalolin da suke fuskanta, wanda tun bayan naɗa shi a muƙamin yake gudanar da irin wannan nasara haɗi da sabbin shugabanin rundunonin sojojin, wanda suke ci gaba da kai wa sojojin da ke bakin fama ziyara lokaci bayan lokaci.

Janar Yahaya ya ƙara da cewa, baya ga ziyarar bai ɗaya da shugabanin sojojin suka kawo wa sojojin a ƙarƙashin shugaban ma’aikatan tsaro a kwanan baya, har wala yau sun gudanar da makamancinta ɗaya bayan ɗaya a yankin.

A hannu guda, ministan tare da tawagarsa sun gudanar da taron sirri tsakaninsu da kwamandojin shalkwatar tsaron Lafiya Dole a lokacin wannan ziyarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *