Rikicin ƙungiyar asiri ya ci mutum shida a Ekiti

Daga BASHIR ISAH

Bayanai daga jihar Ekiti sun tabbatar da mutuwar wasu mutum shida sakamakon rikicin da ya ɓarke a tsakanin ƙungiyoyin asiri a yankin Ikere na jihar.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Sunday Abutu, ya tabbatar wa manema labarai da faruwar haka.

Jami’in ya ce sun gano gawarwakin mutum shida da aka kashe sakamakon rikicin wanda ya auku da sanyin safiyar Lahadi.

Wata majiya daga yankin da abin ya faru ta ce an ji ƙarar harbe-harben bindigogi yayin rikicin lamarin da ya tilasta wa mazauna yankin gudun neman mafaka don tsira da rayuwarsu.

Abutu ya ce waɗanda suka rasa rayukansu ‘yan wata ƙungiyar asiri ne wanda ke hamayya tsakaninsu da takwarorinsu.

Ya ce Rundunar ‘Yan Sandan Ekiti ta cafke wasu mutum uku da ake zargin suna da hannu wajen tada rikicin.

Ya ƙara da cewa bayan da suka samu labarin abin da ke faruwa, jami’ansu tare da haɗin gwiwar sojoji da jami’an tsaron farin kaya da kuma ‘yan bangan Amotekun suka haɗa kai wajen kwantar da tarzomar da ta tashi.

Ya ce suna tsare da mutum uku da aka kama, sannan za su gurfanar da su a kotu da zarar sun kammala bincikensu.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankulansu, tare da ba su tabbacin cewa rundunar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen yaƙi da muggan iri a faɗin jihar.