Ihejirika ya zama ɗan APC

Daga WAKILINMU

Shugaban Kwamitin Riƙo na APC kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya karɓi tsohon Shugaban Rundunar Sojoji Lt.Gen. Oyeabo Azubike Ihejirika (mai murabus) a jam’iyyarsu ta APC.

Manhaja ta gano cewa, tun bayo na Ihejirika ya soma raɓar APC inda sai a wannan lokaci ya tsunduma cikinta a bayyane.

Sanarwa da ta fito ta hannu Daraktan Yaɗa Labarai ga Buni, Mamman Mohammed, ta nuna an gabatar da Gen. Ihejirika a hukumance ga shugaban riƙo na jam’iyyar APC a Juma’ar da ta gabata a bisa jagorancin Gwamnan Jigawa, Alhaji Abubakar Badaru da Hon. Farouk Adamu Aliyu.

Buniya ce, “Zuwan Gen. Ihejirika zai ƙara wa jam’iyyarsu armashi da tagomashi a jihar Abia da ma shiyyar Kudu maso-gabas baki ɗaya.”

Ya ce wannan lokaci ne mai matuƙar muhimmanci ga jam’iyyarsu yadda Gen. Ihejirika tare da wasu ‘yan yankin ke shiga APC don ci gaban jam’iyyar da kuma yankin.

Yana mai cewa, “Muna sa ran ganin ‘yan shiyyar sun ci gaba da shiga APC domin ƙara wa jam’iyyar tagomashi a yankin.”