
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A tsawon sa’o’i 24 da suka gabata gwamnatocin Nijeriya da Afirka ta Kudu na musayar kalamai kan cire jawabin jakadan Nijeriya da ƙasar, Femi Fani-Kayode daga wata ɗaukar kai-tsaye na wani bikin diflomasiyya a birnin Pretoria.
Kakakin shugaban Afirka ta Kudu, Vincent Magwenya, ofishin jakadancin Nijeriya a Pretoria, ya ce hakan wulaƙanci ne ga Mista Fani-Kayode da Nijeriya. Akan haka ne ofoshin, ta shafinsa na X, ya kira Mista Magwenya da “maƙaryaci” kuma “mai tozartawa”.
Ya kuma caccake shi ganin yadda kalaman nasa ka iya haifar da tsaiko ga zaman lafiya da ƙoƙarin sulhun da ke gudana a tsakanin ƙasashen biyu. An bayar da wannan amsa ne kan wallafar da kakakin ya yi akan Fani-Kayode.
A ranar Juma’a ne Ofishin Jakadancin Nijeriyar, ya zargi Fadar Shugaban Ƙasar Afirka ta Kudu da cire gaɓar jawabin Fani-Kayode ta ɗauka kai-tsaye a gidan karɓar baƙi na Sefako Makgatgo da ke Pretoria, inda ya gabatar da takardunsa ga Shugaba Cyril Ramaphosa.
Rahotanni sun ce, Fani-Kayode, wanda kuma shi ne jakadan Nijeriya a ƙasashen Lesotho da Eswatini, ya ce shi kaɗai ne daga cikin jakadu 15 da aka bai wa damar magana aka katse wa jawabi. “Maganar gaskiya, jawabinmu ne kaɗai aka cire,” inji shi.
Akan haka ne Kakakin Afirka ta kudun ya bai wa Fani-Kayode amsa da cewa Hukumar Yaɗa Labaran Afirka ta Kudu (SABC) ce ta jagoranci yaɗa taron, wadda ba fadar shugaban ƙasar ba ne ke gudanar da harkokint, kuma ba ta tsoma mata baki akansu, yana mai zargin jakadan Nijeriya da ƙoƙarin sauya ainihin zance.
Bayan sa’o’i da zargin na Fani-Kayode, SABC ta ɗora wani bidiyo kan jawabinsa a shafinta na yanar gizo. Dangantakar Nijeriya da Afirka ta Kudu ta ɗauki wani salo ne a lokacin da wasu ‘yan ƙasar suka fara kai hare-haren ƙyamar baƙi akan ‘yan Nijeriya da ‘yan wasu ƙasashe da ke zaune a ƙasar kudancin Afirkan.
