Kada ku harbi fusatattun ‘yan Nijeriya – Dalung ga jami’an tsaron shugaban ƙasa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni, Solomon Dalung, ya gargaɗi jami’an hukumomin tsaro da aka ba wa aikin kula da Shugaba Bola Tinubu kan harbin masu zanga-zanga kan zargin farmakar ayarin motocin shugaban a wani masallaci a Abuja.

Wannan cece-kuce ya biyo bayan wasu yaɗa wasu bidiyoyi ne a kafafen soshiyal mediya a ranar Juma’a, bayan kammala sallar Juma’a a Masallacin Shehu Shagari da ke Abuja. Bidiyon ya nuna yadda wasu matasa suka ihun “Bama yi, bama so” da jifa da wasu ababe akan ayarin motocin a lokacin da suke barin masallacin.

Saidai, daga bisani Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da cewa an farmaki ayarin motocin Tinubu, inda mai taimaka wa shugaban, O’tega Ogra ya fitar da wani bidiyo da ke nuna cewa Tinubu ya bar masallacin ne a lokacin da al’umma suka riƙa ɗaga masa hannu ban-girma da jinina.

Da yake tsokaci, Dalung ya gargaɗi waɗanda ke amfani da ƙarfin doka akan masu zanga-zanga da su sake nazari musamman kan yadda hakan yake da tasiri kan muhimman al’amuran ƙasa.

A cewarsa, jami’an tsaron shugaban ƙasa ba arangama suke da ‘yan ta’adda ba, suna fuskantar ‘yan ƙasa ne da ke nuna fushinsu da rashin gamsuwa kan harkokin gwamnati, don haka ya dace a riƙa bin su a sannu ba tare da tsangwama ba.

Ya bayyana cewa, muddin jami’an tsaro suka cigaba da harbin masu zanga-zanga, hakan ka iya rikiɗa zuwa fito na fito tsakanin ɓangarorin biyu da zai iya haifar da asarar rayuka da dukiyoyi.

By Babaji

Leave a Reply