Mataimakin shugaban ƙasar Indonesia ya miƙa takardar murabus bayan takaddama kan shaidar karatunsa

Spread the love

Daga AISHA ASAS

A siyasa, wasu rikice-rikice kan fara ne da tambayoyi game da cancantar shugaba, amma daga bisani su rikide zuwa babban ƙalubalen da zai iya girgiza matsayinsa a gwamnati.

Hakan ne ya faru a ƙasar Indonesia, bayan mataimakin shugaban ƙasar, Gibran Rakabuming Raka, ya miƙa tayin yin murabus daga muƙaminsa a yayin ganawarsa da shugaban ƙasar, Prabowo Subianto, a ranar Talata, 10 ga Nuwamba, 2026.

Kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya ruwaito cewa ganawar tasu ta ɗauki sama da sa’o’i biyu, inda aka tattauna batun takaddamar da ta dabaibaye mataimakin shugaban ƙasar dangane da ingancin takardun shaidar karatunsa.

Sai dai ministan harkokin fadar shugaban ƙasar, Prasetyo Hadi, ya bayyana cewa har zuwa lokacin da yake magana, ba a tabbatar ko shugaban ƙasar ya amince da tayin murabus ɗin ba.

Ya kuma bayyana cewa shugaban ƙasar ya shawarci mataimakinsa da ya ci gaba da amfani da hanyoyin shari’a domin kare ingancin takardun karatunsa.

Gibran, mai shekaru 39, ɗa ne ga tsohon shugaban ƙasar Indonesia, Joko Widodo, wanda ya taɓa jagorantar ƙasar kafin zuwan gwamnatin yanzu.

Takaddamar ta ƙara tsananta ne bayan wani hukuncin Kotun ƙoli da ya shafi takardun karatun da aka gabatar dangane da cancantarsa a zaɓe, lamarin da ya ƙara ƙarfafa kiraye-kirayen da wasu ‘yan majalisa ke yi na a tsige shi.

By ukarofi

Leave a Reply