Yaro ɗan shekara 14 ya ƙirƙiri manhajar kare haƙƙin yara

Spread the love

A yayin da ake ci gaba da kokawa kan matsalolin cin zarafin yara, tauye musu haƙƙoƙi, rashin samun ingantaccen ilimi da kuma ƙarancin hanyoyin tallafa musu a sassa daban-daban na Nijeriya, wani yaro dan shekara 14 ya ba da mamaki bayan ya yi amfani da basirarsa wajen ƙirƙirar wata manhajar zamani da aka tsara domin taimaka wa yara da kuma kare muradunsu.

Matashin mai suna Iɓan Momoh, ɗan asalin Jihar Edo, ya ƙirƙiri wata kafar sadarwa ta zamani mai suna ChildFirst Nigeria, wadda aka tsara domin samar da bayanai, hanyoyin samun tallafi da damammaki ga yara, iyaye, masu kula da yara da kuma hukumomin da ke da alhakin kare haƙƙoƙin yara a ƙasar.

Wannan ƙirƙire-ƙirƙire na matashin ya zo ne a lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan yadda yara da dama ke fuskantar matsaloli da suka haɗa da cin zarafi, talauci, rashin damar samun ilimi, da kuma rashin sanin hanyoyin neman taimako idan aka tauye musu haƙƙoƙi.

Yadda tunanin ƙirƙirar manhajar ya samo asali:

A bayanin da ya yi kan wannan yunƙuri, Iɓan Momoh ya bayyana cewa sha’awarsa ta taimaka wa yara da kare muradunsu ta daɗe tana cikin zuciyarsa, tun kafin ya fara zurfafa cikin harkokin fasahar zamani.

Ya ce tun da farko yana damuwa da irin ƙalubalen da yara ke fuskanta, musamman ta fuskar kariya, ilimi, bunƙasa rayuwa da kuma samun damar cin gajiyar haƙƙoƙin da dokoki suka tanadar musu.

Daga bisani, sha’awarsa ta fasahar zamani ta ba shi damar fara tunanin yadda zai mayar da waɗannan damuwa zuwa wani aiki na zahiri da zai amfani al’umma.

A cewarsa, fasahar sadarwa ta zama wata hanya da zai iya amfani da ita wajen samar da mafita ga wasu daga cikin matsalolin da ke addabar yara.

Rahoton ya bayyana cewa matashin yana da sha’awar ƙirƙirar manhajojin kwamfuta da shafukan yanar gizo, sannan ya taɓa gudanar da wasu ayyukan fasaha kafin ƙirƙirar wannan manhaja.

Haka kuma, ya kammala wani shirin koyar da tsaro a duniyar yanar gizo da ƙungiyar TechstartersAfrica ta shirya a watan Agustan 2026, inda ya samu ƙarin ilimi kan kare bayanai da tabbatar da tsaron masu amfani da fasahar zamani.

By ukarofi

Leave a Reply