Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Abdullahi Sayyadi, Shugaban ƙungiyar Tsofaffin ɗaliban Makarantar Tarauni Special Primary School, wato Tarauni Special Primary School Old Pupils Association (TASPOPA), ya bayyana cewa yanzu kimanin shekaru uku ke nan da suka shirya taron farko na ƙungiyar, kuma tun daga wannan lokaci Ubangiji Ya ba su tunanin tallafa wa yara marayu 46 da kayan Sallah, abinci da sauran abubuwan buƙata domin rage musu raɗaɗin rashin iyayensu.
Shugaban ƙungiyar ya bayyana hakan ne a wajen taron ƙungiyar na farko, wanda aka shirya domin cika shekaru 40 da kammala karatun firamare a makarantar musamman da ke unguwar Tarauni, cikin birnin Kano, a ranar Asabar da ta gabata.
Har ila yau, Sayyadi ya ƙara da cewa ƙungiyar ta bayar da gudunmawa ga makarantar ta hanyar samar da kayan aiki, bututun jan ruwa daga tankin makarantar, gilashin da ke rage zafin rana domin samun wadataccen ruwa, da kuma kayan karatu.
Ya ce, taron na farko ya samu gagarumar nasara, inda tsofaffin ɗaliban makarantar daga Kaduna, Bauchi, Jigawa da sauran sassan ƙasar suka halarta.
Ya bayyana cewa, taron ya zama wata dama ta sada zumunci bayan dogon lokaci, inda wasu mahalarta suka sake haɗuwa da abokan karatunsu a karon farko tun bayan kammala makaranta.
Ya kuma ce an yi amfani da damar wajen karrama mutum 16 da suka taimaka wa makarantar, ciki har da tsofaffin ɗalibai biyu, yayin da sauran mutum 14 suka kasance waɗanda ke tallafa wa makarantar daga waje.
A ƙarshe, Malama Hauwa’u Muhammad Inuwa, mataimakiyar shugabar ƙungiyar tsofaffin ɗaliban makarantar Tarauni, ta ce wannan taro tamkar ibada ne, tun da an yi zumunci.
Ta yabawa dukkan mahalarta taron da waɗanda suka taka rawa wajen ganin an samu nasarar taron na farko.
