2027: Lamiɗo ya musanta iƙirarin Shettima na cewa yana goyon bayan APC

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamiɗo, ya musanta ikirarin Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, na cewa shi da wasu fitattun ’yan siyasa a jihar suna goyon bayan jam’iyyar APC mai mulki.

Lamiɗo ya yi watsi da wannan ikirari ne a wani martani da ya wallafa a shafin Facebook, ƙarƙashin wani bidiyo da shafin DCL Hausa ya wallafa, wanda ke nuna Shettima yana cewa fitattun ’yan siyasar Jigawa, ciki har da tsohon gwamnan, suna tare da APC.

Rubutun da aka wallafa tare da bidiyon ya ƙunshi taken cewa: “Dukkan fitattun mutanen Jihar Jigawa suna tare da mu, har da Sule Lamiɗo.”

Da yake mayar da martani, Lamiɗo ya nuna mamakinsa kan yadda za a danganta shi da APC, yana mai tunatar da cewa bai goyi bayan kafa jam’iyyar ba a shekarar 2014.

A cikin martaninsa da Hausa, ya rubuta cewa: “Ikon Allah. Ban yi APC a 2014 sai yanzu a 2026?”

Haka kuma, Lamiɗo ya yi tsokaci cewa duk da cewa wanda ya yi ikirarin ɗan Kanuri ne, hakan ba abin mamaki ba ne, kafin ya kammala da kalmar Kanuri, “Kattuwunum”, wadda ke nufin ƙarya ko abin da ba gaskiya ba.

Martanin nasa ya nuna cewa ya ƙi amincewa da ikirarin Shettima na cewa yana cikin manyan ’yan siyasar Jigawa da ke goyon bayan jam’iyyar APC.

Bayan wannan martani, tsohon gwamnan ya kuma wallafa wani saƙon ɗaya daga cikin magoya bayansa, wanda ya yi suka ga ikirarin Shettima.

Lamiɗo ya rubuta cewa: “Wani amintaccen mai goyon bayana ne ya rubuta wannan domin kare ni.”

A cikin saƙon, mai suna Auwal Muhammed, ya yi iƙirarin cewa furucin Shettima wani yunƙuri ne na siyasa da nufin danganta Lamiɗo da APC, duk da cewa a cewarsa, tsohon gwamnan bai sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP ba.

Marubucin ya jaddada cewa Sule Lamiɗo ɗan PDP ne kuma yana nan a jam’iyyar, yana mai cewa zai yi kamfen domin nasarar PDP daga sama har ƙasa.

Sai dai kalaman da aka wallafa a matsayin martanin mai goyon bayan Lamiɗo ra’ayinsa ne, yayin da tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya wallafa saƙon ne domin kare matsayinsa kan batun.

By ukarofi

Leave a Reply