Fadar Shugaban Ƙasa ta magantu kan zargin harin ayarin motocin Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Fadar Shugaban Ƙasa ta yi watsi da rahotannin da ke cewa wasu fusatattun matasa sun kai wa ayarin motocin Tinubu hari bayan sallar Juma’a a Masallacin Shehu Shagari da ke Area 1 Garki a Abuja.

Babban Mai taimaka wa Shugaban Ƙasa kan Harkokin Dijital, Dabaru da Soshiyal Mediya, O’tega Ogra ne ya yi watsi da rahotannin, inda ya bayyana bidiyoyin da aka riƙa yaɗawa a Soshiyal Mediya akan al’amarin a matsayin masu ruɗarwa da ke gabatar da aukuwar wani abu daban daga ainihin abin da ya faru yayin barin Tinubu masallacin.

Cece-kucen ya biyo bayan zuwa masallacin da Tinubu ya yi ne a ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, inda aka baza wasu bidiyoyin da ke nuna wasu matasa na ihun nuna adawa da jefa duwatsu akan ayarin wasu motoci da aka ce na Tinubu ne. An ji wasu daga cikinsu na ihun “Ba ma yi, ba ma so”, wanda ke nuna ba sa son sa kuma ba sa goyon bayansa.

An ruwaito cewa, jigon jam’iyyar ADC, Dino Melaye ne ya yaɗa bidiyon, wanda ya gabatar a matsayin hujjar marabtar Tinubu cikin yanayi na nuna rashin goyon baya.

Saidai, Ogra ta kafar X, ya wallafa wani bidiyo da ke nuna yadda shugaban yake ficewa daga masallacin bayan sallar Juma’ar, wanda ke nuna yadda wasu ke ɗaga masa hannu don girmamawa da ƙoƙarin ɗaukar hotuna yayin da yake barin masallacin, yana mai cewa batun cewa an nuna wa Tinubu adawa a lokacin ba gaskiya ba ne.

A cewarsa, wanda aka yi zargin Dino Melaye da wallafawa na da nufin ruɗar da al’umma, inda ya zargi ‘yan adawa da amfani da bayanan ƙarya kan al’amarin, yana mai kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da shi kuma su kasance masu biyayya ga doka da oda yayin da zaɓukan 2027 ke cigaba da ƙaratowa.

By Babaji

Leave a Reply