Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnatin Jihar Katsina ta amince da naɗin shugaban ƙungiyar ‘yan jarida ta ƙasa reshen Jihar Katsina, Kwamred Aminu Garba Dandagoro a matsayin Mai magana da yawun mataimakin gwamnan Jihar Katsina.
Wannan naɗin na ƙunshe a wata takarda da ma’aikatan yaɗa labarai da al’adu da ta fitar ta kuma aikewa mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Faruk LawaL Joɓe.
Kafin wannan muƙamin Kwamred Aminu Garba Dandagoro shine kwantorol na sashin labarai a matakin albashi na GL 13 a gidan talabijin na KTTV a Katsina.
Takardar wanda daraktan yaɗa labarai, Ibrahim Mamman Malumfashi ya sanya wa hannu a madadin kwamishinan yaɗa labarai ya fara aiki nan take.
Ana sa ran zai yi amfani da ƙwarewar sa a aikin jarida wajan ɗaukaka sadarwa a tsarkin ofishin mataimakin gwamna da al’ummar jihar.
Haka kuma ana sa ran a matsayin sa na shugaban ƙungiyar ‘yan jarida reshen jihar zai ƙara masa ƙwarewa wajen tafiyar a aikin sa na jami’in yaɗa labarai na mataimakin gwamna.
