Gwamnatin Nasarawa da Amurka za su raba gidajen sauro na zamani

Spread the love

Daga JOHN D. WADA a Lafia

Gwamnatin Jihar Nasarawa tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Amurka da Shirin kawar da zazzabin cizon sauro na ƙasa (NMEP) za ta raba gidajen sauro masu maganin ƙwari guda miliyan 1.8 ga mazauna jihar domin rage raɗaɗin zazzabin cizon sauro.

Kwamishinan lafiya na Jihar Dakta Gaza Gwamna ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a Lafia.

Yace aikin wani ɓangare ne na sabbin ƙoƙarin gwamnati da abokan ci gabanta na yaƙi da zazzaɓin cizon sauro da kare mazauna jihar musamman yara da mata masu juna biyu.

Ya bayyana cewa zazzaɓin cizon sauro ana yaɗa shi ne ta hanyar cizon sauro masu ɗauke da cutar na Anopheles, kuma yana iya zama mai haɗari ga rayuwa idan ba a yi masa magani yadda ya kamata ba.

Kwamishinan yace gwamnatin jihar ta horar da ma’aikata kusan 9,000 waɗanda za a tura zuwa mazabu 147 a faɗin ƙananan hukumomi 13 na jihar don aikin.

Yace ma’aikatan waɗanda za su sanya kaya ɗauke da tambarin yaƙin zazzaɓin cizon sauro za su ziyarci gidaje daga 15 ga Nuwamba zuwa 21 ga Nuwamba don taswira da rajista, gabanin rabon gidajen sauro da aka shirya daga 6 ga Disamba zuwa 12 ga Disamba.

Yace ƙoƙarin da gwamnatin jihar da abokan hulɗa suka yi ya rage yawan kamuwa da zazzaɓin cizon sauro a jihar daga kashi 25% a shekarar 2018 zuwa kashi 11% a yanzu.

Ya bayyana isar da kiwon lafiya mai sauƙi da mai arha a matsayin babban fifiko na gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule.

A nasa ɓangaren Darakta Janar na lafiyar jama’a na ma’aikatar Dakta Peter Attah yace ƙaramar hukumar Karu ta samu gidajen sauro 300,000, yayin da ƙaramar hukumar Lafia za ta samu 250,000, saboda yawan jama’arsu.

Da take magana a madadin abokan hulɗa, manajan yaƙin shirin Sarkar Samar da lafiya ta duniya – Saye da Samar da Kayayyaki (GHSC-PSM), Patience Ochibe ta ce gidajen sauro suna da darajar fiye da Naira biliyan 6, ban da kuɗin aiki.

Tace haɗin gwiwa da gwamnatin jihar ya fara ne a shekarar 2018, tare da rabon da aka gudanar a baya a shekarar 2022 da kuma 2026.

By ukarofi

Leave a Reply