Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Ministan Aikin Gona da Samar da Abinci, Sanata Abubakar Kyari, tare da manyan masu ruwa da tsaki a ɓangaren noma, za su jagoranci buɗe bikin baje kolin harkokin noma na ƙasa na shekarar 2026, wanda za a gudanar a wajen birnin Abuja.
Gidauniyar Aikin Gona ta ƙasa ta Nijeriya (NAFN) ce ke shirya wannan baje koli a duk shekara, inda ake haɗa manoma, cibiyoyin bincike, masu ƙirƙira sabbin fasahohi, masu samar da ayyuka da sauran masu ruwa da tsaki a dukkan matakan sarƙar samar da amfanin gona da abinci. Taken bikin na bana shi ne: “Gina ingantaccen tsarin samar da amfanin gona da abinci a Nijeriya mai jure sauye-sauye: ƙarfafa manoma, jawo zuba hannun jari da bunƙasa ƙirƙire-ƙirƙire domin tabbatar da wadatar abinci da ci gaban al’umma baki ɗaya.”
Za a gudanar da wannan gagarumin taron na shekara-shekara daga ranar 16 zuwa 20 ga watan Nuwamba, 2026, a filin baje kolin noma na ƙasa da ke kan titin Keffi zuwa Abuja, kilomita 28 daga Abuja, a yankin Tudun Wada, ƙaramar hukumar Karu ta jihar Nasarawa.
Mai kula da harkokin gidauniyar NAFN ta ƙasa, Hajiya Aishatu Rufa’i Ibrahim, ta bayyana cewa baje kolin noma na ƙasa ya kasance ɗaya daga cikin manyan dandamali da ake amfani da su wajen nuna sabbin dabaru da fasahohin noma, kayayyakin amfanin gona, damarmakin zuba jari da kuma hanyoyin magance ƙalubalen da ke addabar harkokin noma da samar da abinci a Nijeriya. Hajiya Aishatu ta ce bikin na bana ya zo a wani lokaci mai muhimmanci, musamman ganin yadda ake ƙara fuskantar matsalolin tabbatar da wadatar abinci, hauhawar kuɗaɗen gudanar da noma, sauyin yanayi, ƙarancin damar samun tallafin kuɗi, rashin isassun injinan noma na zamani da kuma buƙatar ƙarfafa tsarin sarrafa amfanin gona tun daga gona har zuwa kasuwa.
Ta bayyana cewa taron zai samar da wata dama ta musamman ga masu ruwa da tsaki domin musayar ilimi da ƙwarewa, ƙulla yarjejeniyoyin haɗin gwiwa, gano damarmakin zuba jari da kuma inganta manufofin da za su taimaka wajen sauya fasalin harkokin noma a ƙasar nan. Hajiya Aishatu ta yi kira ga ma’aikatun gwamnatin tarayya da na jihohi, hukumomi da hukumomin gudanarwa, ƙananan hukumomi, kamfanoni masu zaman kansu, cibiyoyin hada-hadar kuɗi, abokan hulɗa na ci gaba, cibiyoyin binciken aikin gona, masu zuba jari a harkokin kasuwancin noma, ƙungiyoyin manoma, ƙungiyoyin haɗin gwiwar manoma, manoma masu ƙaramin jari da manyan manoma, da sauran masu ruwa da tsaki, da su fito su halarci wannan gagarumin taro na tsawon kwanaki biyar.
