Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Duk da tabbacin da Ministan Wutar Lantarki, Olasunkanmi Tegbe, ya bayar na cewa za a shawo kan matsalar ƙarancin wutar lantarki da ta daɗe tana addabar Legas, Abuja da wasu jihohi biyu cikin sa’o’i 72, har yanzu ana ci gaba da fama da duhu a jihohin da abin ya shafa, lamarin da ke ƙara jefa masu amfani da wutar cikin mawuyacin hali.
Masu amfani da wutar lantarki sun koka kan yadda matsalar ta ƙara tsananta sakamakon tsananin zafi da ake fama da shi, baya ga hauhawar farashin man fetur da suke amfani da shi wajen samar da madadin wutar lantarki.
A ranar Juma’ar da ta gabata, Tegbe ya fitar da sanarwa inda ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa samar da wutar lantarki zai fara inganta sannu a hankali, bayan an dawo da wasu sassan tashoshin samar da wutar lantarki bakin aiki cikin sa’o’i 48 zuwa 72.
Sai dai maimakon wannan alƙawari ya kawo ƙarshen matsalar, sai ya ƙara haifar da cece-kuce, bayan Kamfanin Mai na ƙasa (NNPC) ya ƙalubalanci bayanan da ministan da Hukumar Kula da Ayyukan Wutar Lantarki Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (NISO) suka bayar na cewa ƙarancin iskar gas ne ya haddasa rashin wutar.
A ranar Alhamis ɗin da ta gabata, NISO ta bayyana cewa ƙarancin wutar da ake samarwa ya samo asali ne daga ƙarancin iskar gas da ake kai wa tashoshin samar da wutar lantarki ta gas, tare da raguwar ruwan da ke shiga madatsun ruwa da ake amfani da su wajen samar da wutar lantarki.
Hukumar ta ce, ƙarancin iskar gas ya taƙaita ikon tashoshin samar da wutar lantarki ta gas wajen yin aiki gwargwadon ƙarfinsu, yayin da raguwar ruwan da ke shiga madatsun ruwa ta rage ƙarfin samar da wutar lantarki a tashoshin da ke amfani da ruwa.
A nasa ɓangaren, Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, ya danganta matsalar da aikin gyaran da ake gudanarwa a tashar samar da wutar lantarki ta Egbin, wadda ke samar da kusan kashi 16 cikin 100 na wutar da ake aikawa babban layin rarraba wutar lantarki na ƙasa. Ya kuma danganta matsalar da ƙarancin iskar gas ga tashoshin samar da wuta da kuma lalata wasu layukan isar da wutar lantarki da gangan. Ya ce saboda wannan gibi da aka samu, masu kula da babban layin rarraba wutar lantarki sun fara rage yawan wutar da ake bai wa wasu yankuna domin tafiyar da ƙarancin wutar da ake da ita.
Ministan ya ƙara da cewa lalata muhimman layukan isar da wutar lantarki ya hana amfani da wasu hanyoyin da za a iya bi wajen isar da wutar a madadinsu.
Sai dai Kamfanin Mai na ƙasa (NNPC) ya yi watsi da waɗannan bayanai ta bakin Babban Jami’insa mai kula da yaɗa labaran kamfani, Andy Odeh. Odeh ya ce cibiyar samar da ababen more rayuwa na iskar gas ta kamfanin NNPC, wato NNPC Gas Infrastructure Company Limited (NGIC), na ci gaba da aiki yadda ya kamata, kuma tana da ƙarfin isar da iskar gas zuwa tashoshin samar da wutar lantarki a Nijeriya. Ya kuma bayyana cewa bayanan ayyukan kamfanin NGIC ba su nuna akwai wata matsala ta jigilar iskar gas a cikin hanyoyin sadarwarsa da za ta iya bayyana raguwar wutar lantarkin da ake fuskanta a halin yanzu ba.
A cewarsa, samar da iskar gas ya ƙaru da kusan kashi 10 cikin 100 tun daga farkon shekarar 2026 zuwa yanzu. Ya jaddada cewa samuwar iskar gas ba ita ce matsalar ba, yana mai cewa akwai buƙatar bambance tsakanin samar da iskar gas, jigilar ta, yarjejeniyoyin kasuwanci da kuma ainihin yawan iskar gas ɗin da masu amfani ke karɓa.
Wannan matsala ta tilasta wa wasu kamfanonin rarraba wutar lantarki rage yawan wutar da suke bai wa abokan hulɗarsu, lamarin da ya jawo ƙorafe-ƙorafe daga masu amfani da wutar.
Haka kuma, Kamfanin Isar da Wutar Lantarki na Nijeriya (TCN) ya yi watsi da iƙirarin kamfanin rarraba wutar lantarki na Ikeja Electric na cewa rashin daidaiton babban layin wutar lantarki ne ya haddasa matsalar. TCN ta bayyana cewa aikinta shi ne isar da adadin wutar da aka samar zuwa wuraren da ake buƙatarta, ba wai samar da wutar da ba a samar ba. Kamfanin ya jaddada cewa ƙarancin wutar da ake samarwa ne ya haddasa matsalar, ba gazawar hanyoyin isar da ita ba.
Masana da suka zanta da manema labarai sun bayyana cewa wannan taƙaddama tsakanin hukumomin da ke da alhakin samarwa da isar da wutar lantarki na nuna gazawa da matsaloli da suka dabaibaye tsarin samar da wutar lantarki a Nijeriya.
Wani masani kan harkokin makamashi, Rasheed Adeleke, ya nuna takaicinsa kan cece-kucen da ake yi ba tare da wata buƙata ba game da ƙarancin iskar gas a ƙasar. Adeleke ya ce idan aka yi la’akari da yawan iskar gas da Nijeriya ke da shi da kuma tarin ma’adinan da take da su, babu dalilin da zai sa ƙasar ta riƙa fama da ƙarancin iskar gas da kuma talaucin makamashi.
Ya bayyana cewa yawan ɗora wa juna laifi da takaddamar da ke faruwa tsakanin hukumomin gwamnati abin takaici ne, kuma da ba za a fuskance su ba idan ana gudanar da muhimman fannoni kamar makamashi bisa ƙa’idojin da doka ta tanada da kuma ingantattun matakan da ake bi a duniya. Ya ƙara da cewa, wannan musayar zargi ta sake jefa ƙasar cikin wani sabon yanayin samun wutar lantarki ba bisa ƙa’ida ba, inda wutar ke zuwa lokaci-lokaci tare da yawan ɗaukewa.
A wani taron masana harkokin makamashi da ƙungiyar Tsofaffin ɗaliban Makarantar Kasuwanci ta Harvard da ke Nijeriya ta shirya a Legas kwanan nan, Babban Mai Bai wa Gwamnati Shawara kan Fasaha a fannin Haƙo Mai da Iskar Gas, Gbite Adeniji, ya bayyana cewa hanyar magance matsalar ƙarancin kuɗaɗen da ke addabar ɓangaren wutar lantarki ita ce gwamnati ta biya basussukan da ake bin ta tare da samar wa Hukumar Sayen Wutar Lantarki ta Nijeriya (NBET) ingantaccen tsarin tallafin kuɗi.
A cewarsa, gazawar masu samar da iskar gas wajen karɓar kuɗin da ake bin su kan iskar gas ɗin da suke kai wa tashoshin samar da wutar lantarki na shafar dukkan sassan tsarin samar da wutar lantarki a ƙasar. Ya ce babban abin dubawa shi ne ko masu sayen iskar gas suna da ƙarfin biyan kuɗin da suke karɓar iskar gas ɗin da suka saya. Ya bayyana cewa idan aka magance wannan matsala, za a ga yadda yawan buƙata da amfani da iskar gas za su ƙaru sosai.
A nata ɓangaren kuma, Babbar Daraktar ƙungiyar Kamfanonin Samar da Wutar Lantarki (APGC), Dakta Joy Ogaji, ta danganta matsalar ƙarancin wutar da tarin basussukan da ake bin hukumomi da kamfanonin da ke cikin tsarin samar da ita. Ta bayyana cewa gwamnati na bin kamfanonin samar da wutar lantarki (GenCos) bashin da ya kai kusan Naira tiriliyan 6.8, yayin da masu samar da iskar gas kuma ake bin su bashin kusan Naira tiriliyan 3.3.
