Kasafin 2027: Bashir Galadima ya yaba wa shugabannin ƙananan hukumomin Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Hon. Alhaji Bashir Abubakar Galadima, Hadimin Gwamnan Jihar Kano a Ma’aikatar ƙananan Hukumomi, ya bayyana jin daɗinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kuɗin shekarar 2027 na ƙananan hukumomi 44 na jihar.

Galadima ya bayyana hakan ne bayan zaman gyaran kasafin kuɗin da aka gudanar a ƙarƙashin ma’aikatar, inda ya yaba wa dukkan shugabannin ƙananan hukumomi, daraktocin mulki, daraktocin kuɗi da ma’aji, da kuma shugabannin sassa bisa haɗin kan da suka nuna wajen ganin an kammala aikin cikin nasara.

Ya ce an shigar da dukkan dokoki da ƙa’idojin da Gwamnatin Jihar Kano ta bayar domin tabbatar da cewa kasafin kuɗin na 2027 ya kasance ba tare da wata matsala ba, domin kauce wa samun gibi a ayyukan raya ƙasa da aka tsara wa al’umma a faɗin jihar.

Ya ƙara da cewa kasafin kuɗi hasashe ne, ba kuɗi a ƙasa ba. Hasashe ne na abin da ake sa ran ƙananan hukumomi za su tara a matsayin kuɗaɗen shiga, domin haɗa kai wajen aiwatar da ayyukan yau da kullum da kuma ayyukan da al’umma za su amfana da su.

A ƙarshe, a madadin Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, Hon. Bashir Abubakar Galadima ya yi kira ga ƙananan hukumomi 44 da su ƙara zage damtse wajen tara kuɗaɗen shiga fiye da yadda suke yi a baya.

Ya jaddada cewa shigar kuɗaɗen shiga cikin asusun baitulmalin ƙananan hukumomi ne zai ba su fifiko da kuma damar samun ƙarin tallafi daga Gwamnatin Tarayya.

By ukarofi

Leave a Reply