Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Femi Gbajabiamila, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, ya sanar da sauya tsarin sashen yaɗa labarai da sadarwa na kwamitin yaƙin neman zaɓen Shugaba Bola Tinubu na jam’iyyar APC.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, Gbajabiamila ya ce daga yanzu mutum uku ne kawai aka amince su riƙa magana a madadin kwamitin.
Mutanen su ne Sanata Abdulaziz Yari, Darakta-Janar na kwamitin; Dele Alake, Ministan Ma’adanai, wanda shi ne kakakin kwamitin; da Mohammed Idris, Ministan yaɗa labarai.
Ya bayyana cewa duk sauran waɗanda aka sanar a baya a matsayin masu magana da yawun kwamitin za su koma ƙarƙashin sashen yaɗa labarai da sadarwa a matsayin mambobi.
Gbajabiamila ya ce matakin na da nufin tabbatar da tsari, haɗin kai da ingancin saƙonnin da kwamitin ke isarwa ga jama’a.
Ya kuma buƙaci gidajen rediyo da talabijin su lura da sabon tsarin, inda ya ce kwamitin zai riƙa tura mutanen da suka dace domin halartar shirye-shiryensu a duk lokacin da buƙata ta taso.
