Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) na iya duba rikicin shugabancin jam’iyyar ADC a wani taronta da ake sa ran gudanarwa mako mai zuwa, bayan dawowar shugabanta daga wata tafiyar aiki.
Kwamishinan INEC na ƙasa, Malam Mohammed Kudu Haruna, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta wayar tarho, inda yake amsa tambayoyi kan ko hukumar ta karɓi sahihin kwafin hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya shafi taƙaddamar shugabancin jam’iyyar. Haruna, wanda shine shugaban kwamitin hukumar mai kula da yaɗa bayanai da wayar da kan masu zaɓe, ya ce har zuwa daren ranar Talata, hukumar ba ta karɓi sahihin kwafin hukuncin kotun ba, duk da cewa ta samu takardar ɗaukaka ƙara da ADC ta shigar, tare da buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin. Ya ce, “Ban da masaniyar cewa mun karɓi sahihin kwafin hukuncin. Har yanzu ba mu karɓe shi ba.”
Ya ƙara da cewa takardun da suka shiga hannun hukumar su ne na ɗaukaka ƙarar da ADC ta shigar da kuma buƙatar dakatar da aiwatar da hukuncin, amma ba sahihin kwafin hukuncin kotun ba. Da aka tambaye shi lokacin da hukumar za ta iya yanke matsaya bayan karɓar takardar hukuncin, Haruna ya bayyana cewa sai an gudanar da taron kwamishinonin hukumar kafin a cimma matsaya kan batun.
Ya ce a halin yanzu shugaban INEC yana wata tafiyar aiki, don haka ba zai samu damar halartar taron da hukumar ta tsara gudanarwa ba. A cewarsa, hukumar kan gudanar da tarurrukanta a ranar Alhamis, duk da cewa a wasu lokuta tana yin taro a ranar Talata. Haruna ya ce ana sa ran shugaban hukumar zai dawo ranar Lahadi, lamarin da ka iya ba da damar gudanar da taron kwamishinonin a ranar Talata ko Alhamis na mako mai zuwa.
Da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar taron ya gudana a ranar Talata mai zuwa, ya amsa da cewa hakan na iya yiwuwa, domin ana sa ran shugaban hukumar zai dawo kafin lokacin. Sai dai ya yi gargaɗin cewa bai kamata a ɗauki waɗannan ranaku a matsayin tabbatattu ba, domin ba zai iya tabbatar da takamaiman lokacin da hukumar za ta gudanar da taro ko kuma yanke matsaya kan rikicin ba.
