Fasto ya nemi afuwa bayan rera waƙar kamfen ɗin Obi a coci

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fasto na Cocin Katolika, Rabaran Finbarr Chukwu, ya nemi afuwar al’umma bayan wani faifan bidiyo da ya nuna shi yana rera waƙar kamfen ɗin siyasa da ake dangantawa da Peter Obi a yayin gudanar da ibada a coci ya tayar da ƙura a kafafen sada zumunta.

Chukwu, wanda ke aiki a Makarantar Sakandare ta St. Dominic da ke Ugiri, a ƙaramar hukumar Isiala Mbano ta Jihar Imo, ya gabatar da uzurinsa ne ta wata wasiƙar ƙarin haske mai kwanan wata 4 ga Nuwamba, 2026. A cikin wasiƙar da ya aikawa Bishop ɗin Cocin Katolika na Diocese na Okigwe, Rabaran Solomon Amatu, da sauran limaman cocin, mabiya addinin Katolika da kuma al’umma baki ɗaya, faston ya danganta abin da ya faru da wani yanayi na bazata a yayin bikin godiya da wani iyali suka shirya, wanda wasu abokan hulɗarsu a harkokin kamfen ɗin siyasa suka halarta.

Ya bayyana cewa bayan wasu daga cikin mahalarta taron sun fara rera waƙoƙin kamfen na siyasa, shi ma ya bi su ba tare da shiri ba, na ɗan lokaci kaɗan, ba tare da zurfafa tunanin abin da hakan ka iya haifarwa ko yadda jama’a za su fassara matakin nasa ba. A cewarsa, daga baya ne ya fahimci illar abin da ya aikata, inda ya tunatar da mahalarta taron muhimmancin kiyaye martaba da tsarkin ayyukan coci, ta hanyar ware harkokin siyasa daga bukukuwan addini.

Faston ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda ɓangaren taron da ya yi wannan jan hankali bai bayyana a cikin faifan bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumunta ba, lamarin da ya ce ya sa mutane suka fahimci abin da ya faru ta wani ɓangare kawai. Chukwu ya ƙara jaddada cewa bai shiga rera waƙar ne saboda wata manufa ta siyasa ko goyon bayan wata jam’iyya ba. Sai dai ya amince cewa matakin nasa zai iya sa jama’a su ɗauka cewa yana goyon bayan wani ɗan takara ko wata jam’iyyar siyasa.

A cikin wasiƙar, ya ce, “Duk da haka, na amince cewa a matsayina na fasto, yadda mutane suke kallon abin da muka aikata yana da matuƙar muhimmanci. Mabiya addini suna da kyakkyawan dalilin sa ran cewa ba wai kawai za mu kasance masu tsaka-tsaki a harkokin siyasa ba, har ma da nuna halayen da ba za su bar wata shakka ba kan jajircewarmu wajen bin koyarwar Coci da kuma aiwatar da manufarta.”

Ya ƙare da amincewa da cewa a matsayinsa na shugaban addini, ya kamata ya fi kula da duk wani abu da zai iya haifar da zargin cewa ya karkata ga wata jam’iyyar siyasa ko ɗan takara, domin kiyaye mutunci da martabar cocin da kuma amincewar mabiya addini.

By ukarofi

Leave a Reply