Nijeriya za ta maye tsofaffin kayan lantarki cikin wata biyu, inji minista

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta shirya fara sauya tsofaffin kayayyakin more rayuwa da ke cikin babban tsarin samarwa da rarraba wutar lantarki na ƙasa nan da wata ɗaya zuwa biyu masu zuwa.

Ministan Lantarki, Joseph Tegbe, ne ya bayyana hakan, inda ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana bayar da cikakken goyon baya ga shirin da gwamnati ta ƙaddamar domin magance matsalolin da suka dabaibaye ɓangaren wutar lantarki. Tegbe ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na TVC. Ministan ya ce, gwamnatin za ta fara aikin sauya tsofaffin kayayyakin lantarki a faɗin ƙasa cikin watanni biyu masu zuwa. Ya ce, “Don haka, cikin wata caya zuwa biyu masu zuwa, za mu fara sauya kayayyakin more rayuwa a faɗin tsarin rarraba wutar lantarkin ƙasa. Shugaba Tinubu yana matuƙar goyon bayan dukkan matakan da muke cauka.”

Ministan ya bayyana cewa babbar matsalar da ke addabar ɓangaren wutar lantarki a Nijeriya ita ce raunin tsarin isar da wuta daga tashoshin samarwa zuwa wuraren rarrabawa, yana mai cewa wasu layukan lantarki da ake amfani da su a ƙasar sun shafe kusan shekaru 50 suna aiki. Ya ce ma’aikatarsa ta fara gudanar da cikakken binciken fasaha a dukkan sassan ɓangaren wutar lantarki, domin gano kayayyakin da suka lalace ko suka tsufa waɗanda ke buƙatar gyara ko sauyawa, tare da tabbatar da cewa ana ware kuɗaɗe zuwa wuraren da suka fi buƙata.

A cewarsa, an shafe kusan wata guda ana gudanar da binciken, kuma tuni an fara samun sakamakon da zai taimaka wajen tsara matakan gyara matsalolin. Ya ƙara da cewa, binciken ya gano matsaloli a wasu muhimman kayayyakin lantarki, ciki har da hasumiyoyin ɗaukar wayoyin wuta, na’urorin kariya daga matsalar wutar lantarki da kuma na’urorin haɗa wayoyin isar da lantarki.

Tegbe ya bayyana cewa akwai wuraren da matsalar take a hasumiyoyin ɗaukar wayoyin wuta, wasu kuma na’urorin kariya ne suka lalace, yayin da a wasu wuraren matsalar take cikin na’urorin haɗa layukan lantarki. Ya ce, “Abin da ba za mu so ba shi ne mu fara kashe kuɗi wajen sauya na’urorin kariya, alhali ainihin matsalar tana cikin na’urar haɗa layin lantarki. Yanzu haka muna samun cikakken haske kan inda matsalolin suke.”

By ukarofi

Leave a Reply