Yadda matsalolin bututun mai suka hana Nijeriya samar da ganga miliyan 42.6 a 2025

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Nijeriya ta kasa samarwa ko fitar da gangar ɗanyen mai da kuma man da ake samu tare da shi, wato Condensate kimanin miliyan 42.55 a shekarar 2025, sakamakon matsalolin bututun mai da sauran tangarɗar ayyukan samar da mai, inda adadin man ya kai kimar kasuwa ta kusan dala biliyan 2.97.

Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Nijeriya (NUPRC) ce ta bayyana hakan a cikin rahotonta na shekara-shekara na 2025, inda ta ce matsalolin sun janyo tsaikon samar da gangar mai 116,563 a kullum. Hukumar ta danganta mafi yawan matsalolin da lalacewa ko dakatar da aiki a manyan bututun jigilar mai, ciki har da bututun Trans Niger, Nembe Creek da Trans Forcados. Ta kuma bayyana cewa lalacewar kayan aiki, ayyukan gyaran bututu da jinkirin ɗora mai a cikin jiragen dakon mai a tashoshin fitar da mai zuwa ƙasashen waje sun taimaka wajen haddasa wannan matsala.

A fannin man fetur, tsaikon samar da mai na nufin ɗanyen man da kamfanonin haƙo mai suka kasa samarwa ko fitarwa a lokacin da aka tsara, sakamakon matsalolin aiki ko lalacewar ababen more rayuwa. Ko da yake ana iya samun damar samar da wani ɓangare na man daga baya, tsawaitar irin waɗannan matsaloli na iya rage kuɗaɗen shiga daga fitar da mai zuwa ƙasashen waje a lokacin da ya kamata, tare da rage kuɗaɗen shigar gwamnati.

Wani nazari da aka gudanar kan alƙaluman hukumar na kowane wata ya nuna cewa watan Oktoba ne ya fi kowanne yawan tsaikon samar da mai, inda aka samu tsaikon gangar mai 172,761 a kullum. Sai watan Maris da gangar mai 169,856, sannan Disamba da gangar mai 169,786 a kullum.

A gefe guda kuma, watan Yuli ne ya fi kowanne ƙarancin tsaikon samar da mai, inda aka samu gangar mai 25,780 kacal a kullum. Alƙaluman watan Oktoba sun haura na watan Yuli da kusan kashi 570 cikin ɗari, abin da ke nuna girman matsalolin da suka kawo tsaikon samar da mai a shekarar. An ƙididdige kimar dala biliyan 2.97 ne ta hanyar amfani da matsakaicin farashin ɗanyen man Nijeriya mai suna Bonny Light a kowane wata, tare da kwatanta shi da adadin gangar man da aka kasa samarwa ko fitarwa.

Rahoton nazarin tattalin arziki da hasashen shekarar 2026 na kamfanin United Capital ya nuna cewa matsakaicin farashin gangar ɗanyen man Bonny Light ya kasance dala 70.88 a shekarar 2025, idan aka kwatanta da dala 82.40 a shekarar 2024. Hakan na nufin farashin ya ragu da kashi 14 cikin ɗari.

Sai dai hukumar ta yi ƙarin haske cewa kimar dala biliyan 2.97 ba ta nufin tabbatacciyar asarar kuɗaɗen shiga da gwamnatin tarayya ko kamfanonin mai suka yi ba. Hasali ma, adadin ya nuna kimar man ne a kasuwa, domin akwai yiwuwar a iya samar da wani ɓangare na man daga baya.

Hukumar NUPRC ta ce matsalolin dakatarwar aiki a manyan bututun jigilar mai ne suka fi haddasa tsaikon samar da mai a shekarar da ake magana a kai.

By ukarofi

Leave a Reply