Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Babban Sakataren Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, Alhaji Abba A. ɗanguguwa, ya bayyana taron haɗuwar tsofaffin ɗaliban Makarantar Firamare ta Tarauni Special, ajin 1986, a matsayin taro mai albarka, wanda ke ƙarfafa zumunci da kuma samar da mu’amala mai ma’ana wajen bunƙasa ci gaba.
Alhaji ɗanguguwa, wanda shi ma tsohon ɗalibi ne a makarantar, ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a wajen taron tsofaffin ɗaliban da kuma gabatar da tallafin bunƙasa makarantar, wanda aka gudanar a harabar makarantar da ke Tarauni.
Ya ƙara da cewa taron ya haɗa tsofaffin ɗalibai daga wurare daban-daban, waɗanda a wani lokaci suka yi karatu a aji guda, amma suka rabu na tsawon shekaru, kafin daga bisani su sake haɗuwa.
Ya ce kowannensu ya zo da irin ƙwarewa da ilimin da ya samu a fannoni daban-daban na sana’o’insa domin yin mu’amala da juna da kuma musayar ra’ayoyi.
“A haƙiƙanin gaskiya, wannan haɗuwa ce da ta ba mu damar duba irin ci gaba da nasarorin da aka samu cikin shekaru 40 da suka gabata. Haka kuma, lokaci ne na addu’a da tuna baya,” inji shi.
Ya bayyana cewa irin wannan taro kira ne ga ƙananan yara masu tasowa da ke karatu a makarantar, domin su ga irin nasarorin da manyansu da suka gabace su suka samu a rayuwa, su kuma yi koyi da su wajen zama nagartattun mutane a cikin al’umma.
Da yake magana kan muhimmancin ilimi, Babban Sakataren ya ce babu shakka ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma.
Sai dai ya bayyana damuwarsa kan yadda ingancin ilimi ke fuskantar ƙalubale sakamakon matsaloli da tabarbarewar tattalin arziki, yana mai cewa ingancin ilimin da ake samu a yanzu ba ya kai na shekarun baya.
Duk da haka, ya ce gwamnatocin baya da na yanzu suna ƙoƙarin ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da ingantaccen ilimi ga yara.
Ya ce Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Kabir Yusuf, ta ɗauki matakai masu inganci wajen bunƙasa harkokin ilimi, musamman ta hanyar sanya dokar ta-ɓaci a ɓangaren ilimi, wanda ya ce ana samun ci gaba sosai sakamakon hakan.
Ya bayyana matakan a matsayin abin a yaba.
A yayin taron, an kuma karrama wasu daga cikin tsofaffin ɗaliban ajin 1986 da takardun shaidar yabo bisa gudummawar da suke bayarwa wajen tallafa wa makarantar.
