Kwamishinan gidaje na Kano ya yaba da taron masu harkar gidaje da filaye

Spread the love

Daga IBBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Kwamishinan Gidaje da Bunƙasa Birane na Jihar Kano, Arch. Ibrahim Yaƙub Adamu Garko, ya bayyana taron masu harkar gidaje da filaye na Kano, wato Real Estate Eɗpo, a matsayin muhimmin taro da ya dace da matsayin Jihar Kano a Nijeriya da ma duniya baki ɗaya.

Arch. Garko ya ce taron ya haɗa ’yan kasuwa da wakilan gwamnati domin tattaunawa kan harkokin gine-gine, gidaje da sauran abubuwan da suka shafi fannin Real Estate.

Ya bayyana cewa Allah ya albarkaci Kano da ci gaba sosai a fannin gine-gine, inda darajar filaye a wasu yankunan jihar ta kai har ma ta zarce ta Abuja.

Ya ce saboda haka, ya dace a riƙa gudanar da irin waɗannan taruka domin jama’a su fahimci irin matakan da gwamnati ke ɗauka, sannan masu zuba jari (developers) su bayyana buƙatunsu ga gwamnati, domin haɗa hannu wajen rage matsalar ƙarancin gidaje a ƙasar nan.

“Manufar ita ce a samar da gidaje masu yawa waɗanda kowa zai iya saya cikin sauƙi, sannan a tsaftace harkar domin dakile hanyoyin da ba su dace ba a harkokin gidaje,” in ji shi.

Kwamishinan ya ce ya ji daɗin ganin yadda ’yan Jihar Kano suka fara shiga harkar samar da gidaje, yana mai fatan za a ci gaba da gudanar da irin wannan taro a duk shekara domin tattauna tare da warware matsalolin da ke addabar harkar gidaje, manya da ƙanana.

Ya ƙara da cewa Gwamnatin Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta fito da sabbin tsare-tsare a fannin gidaje.

Ya bayyana cewa ɗaya daga cikin matakan da gwamnatin ta ɗauka shi ne raba Hukumar Tsara Birane da Filaye ta Jihar Kano (KNUPDA) zuwa hukumomi biyu.

Ya ce ɗaya daga cikin hukumomin za ta riƙa bayar da izinin gini cikin sauƙi da sauri, yayin da ɗayar kuma za ta riƙa sa ido da kulawa domin tabbatar da cewa an bi ƙa’idojin da aka gindaya wajen bayar da izinin ginin.

By ukarofi

Leave a Reply