Mele Kyari ya bayyana a gaban Majalisar Dattawa kan zargin ɓatar tiriliyan N210 na NNPCL

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Babban Manajan Daraktan Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPCL), Mele Kyari, ya yi watsi da zargin da Majalisar Dattawa ta yi na cewa akwai kuɗaɗen da ba a san inda suka shiga ba har Naira tiriliyan 210, yana mai cewa babu kuɗin da aka yi asara a lokacin da yake jagorantar kamfanin.

Rahoton News Point Nigeria ya bayyana cewa Kyari ya ce zarge-zargen da suka shafi bayanan kuɗaɗen kamfanin tsakanin shekarar 2017 zuwa 2023 sun samo asali ne daga rashin fahimtar wasu bayanan lissafin kuɗi da kuma yadda aka rubuta su.

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata lokacin da ya gurfana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Asusun Jama’a, wanda ke binciken tambayoyin da Ofishin Babban Mai Binciken Kuɗi na Tarayya ya gabatar dangane da bayanan kuɗaɗen NNPCL na shekarun da abin ya shafa.

Da yake karin bayani kan batun, Kyari ya ce kamfanin ya yi ƙoƙarin aiwatar da shawarwarin Majalisar Dokoki ta ƙasa, lamarin da ya haifar da ci gaba da zuba jari da bunƙasa ɓangaren kasuwancin man fetur na cikin gida domin amfanin ƙasa.

“Na yi matuƙar alfahari da yadda muka yi wa wannan kamfani hidima gwargwadon iko. Ina nan da aminci ga ƙasata, kuma ban aikata wani abu da gangan domin aikata ba daidai ba,” inji shi.

Dangane da kuɗaɗen da aka biya Hukumar Tara Haraji ta Tarayya (FIRS), Kyari ya bayyana cewa kuɗaɗen na kuɗaɗen rajista ne, yana mai cewa bambance-bambancen da aka samu sun shafi yadda aka shigar da bayanan ne. Ya kuma ce naira biliyan 2.9 da ake magana a kai kuɗaɗen da doka ta tanada ne.

Game da zargin kashe naira biliyan biyar wajen sauya sunan NNPCL, tsohon shugaban kamfanin ya ce Majalisar Dokoki ta ƙasa ce ta aiwatar da sauya sunan, yana mai cewa ba a biya wani kuɗi ba wajen gudanar da wannan aiki.

Daga nan ne Kyari ya miƙa rahotonsa ga kwamitin.

A nasa jawabin, Shugaban kwamitin ya ce akwai batutuwa 23 da aka gabatar wa kwamitin, amma ɗaya ko biyu ne kawai suka shafi tsohon shugaban NNPCL.

Ya ce za a rarraba rahoton ga mambobin kwamitin domin su duba shi, tare da bayyana cewa kwamitin na iya gayyatar waɗanda abin ya shafa da kuma Babban Mai Binciken Kuɗi na Tarayya domin ƙarin bayani idan buƙatar hakan ta taso.

Shugaban kwamitin ya ce sun amince da uzurin Kyari na rashin halartar zaman da suka gabata, kuma za su yi nazari kan alkaluman kuɗaɗen.

Bayan haka, kwamitin ya sallami Kyari, yana mai cewa hakan na jiran kammala bincikensa.

Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Asusun Jama’a ya fara binciken batun waɗannan alkaluma masu cike da saɓani ne a watan Yunin 2025, bayan gano bambance-bambance a cikin bayanan kuɗaɗen NNPCL da aka tantance na shekarun 2017 zuwa 2023.

Alƙaluman sun haɗa da naira tiriliyan 103 da aka rubuta a matsayin kuɗaɗen da suka taru a matsayin basussuka, da kuma naira tiriliyan 107 da aka lissafa a matsayin wasu kuɗaɗen da ake bin wasu mutane ko hukumomi.

Kwamitin ya sha yin watsi da bayanan da kamfanin ya gabatar a baya, yana mai cewa dole ne a yi cikakken bayani kan yadda aka samu waɗannan alkaluma.

A watan Maris na 2026, kwamitin ya gayyaci Kyari da wasu tsoffin jami’an kamfanin domin su yi bayani kan kuɗaɗen. Daga baya, a watan Yunin 2026, ya bayar da umarnin a kama Kyari bayan ya kasa halartar zaman da aka shirya.

Sai dai tsoffin jami’an NNPCL sun musanta cewa kuɗaɗen sun ɓace, suna mai cewa alkaluman naira tiriliyan 210 sun samo asali ne daga kuskuren fahimtar bayanan kuɗaɗen kamfanin.

By ukarofi

Leave a Reply