Kwastamomi sun zargi Moniepoint da jan ƙafa wajen dawo musu da kuɗaɗensu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Juyin-juya-halin fasahar hada-hadar kuɗi a Nijeriya ya sauƙaƙa tare da hanzarta aika kuɗi da karɓar su, amma ƙorafe-ƙorafen da ke ƙaruwa kan yadda ake kasa dawo wa mutane da kuɗaɗen da suka salwanta sakamakon damfara ta intanet, na ƙara jefa tambayoyi kan yadda kamfanonin hada-hadar kuɗi ke kare haƙƙin kwastomominsu da kuma ɗaukar alhakin asarar da suka yi.

A cikin wannan rahoto na musamman na ranar Litinin, an yi nazari kan halin da wasu kwastomomi biyar suka ce sun shiga, bayan sun tura kuɗaɗensu zuwa asusun wasu da ake zargin ’yan damfara ne ta hanyar amfani da asusun Moniepoint. Waɗannan mutane sun bayyana cewa duk ƙoƙarin da suka yi na ganin an dawo musu da kuɗaɗensu ya ci tura, inda abin da suke samu kawai shi ne uzurori, bayanai masu sarƙaƙiya na fasaha da kuma alƙawarin cewa ana gudanar da bincike.

Manyan kamfanonin hada-hadar kuɗi ta intanet, ciki har da Moniepoint da OPay, sun fuskanci suka kan zargin raunin tsarin da suke amfani da shi wajen magance matsalolin damfara.

ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ake ƙorafi a kai shi ne yadda ake buƙatar umarnin kotu kafin a iya riƙe kuɗaɗen da aka tura zuwa asusun waɗanda ake zargi ko kuma a dawo da su.

Ga talakawa da sauran masu ƙaramin ƙarfi, samun irin wannan umarnin kotu na iya cin kuɗi da kuma ɗaukar lokaci mai tsawo. Misali, wani ɗan kasuwa a jihar Enugu ya fuskanci kashe kuɗin lauya har Naira 120,000 a ƙoƙarinsa na dawo da Naira 25,100 da ya tura bisa kuskure.

Haka kuma, ana samun ƙorafe-ƙorafe cewa ko da kwastomomi sun gabatar da takardun da ake buƙata ko kuma umarnin kotu, wani lokaci ƙoƙarin dawo da kuɗaɗen kan tsaya cak a sassan kula da bin ƙa’idoji da yaƙi da damfara na kamfanonin, lamarin da ke barin waɗanda aka cutar cikin mawuyacin hali na rashin kuɗi.

Yadda kwastomomi biyar suka yi asarar kuɗaɗensu:

Ga Nosa David, mazaunin jihar Edo, matsalar ta fara ne lokacin da ya tura Naira 175,000 daga asusunsa na Moniepoint zuwa wani asusun Moniepoint na wani mai sayar da takalma ta intanet a birnin Benin. A cewarsa, bayan mutumin ya karɓi kucin, sai ya ɓace, ya daina amsa kiraye-kirayen waya da saƙonnin da yake aika masa.

David ya ce nan take ya kai rahoton lamarin tare da gabatar da cikakkun bayanan cinikin kuɗin, amma bayan shafe makonni da watanni, har yanzu ba a dawo masa da kuɗinsa ba. Ya bayyana cewa, duk lokacin da ya tuntuɓi kamfanin domin jin halin da ake ciki, abin da ake yi masa shi ne gabatar da bayanan fasaha da kuma tabbatar masa cewa ana gudanar da bincike kan lamarin. Ya kuma nuna rashin fahimtarsa kan dalilin da zai sa a kasa gano tare da warware matsalar cinikin kuɗi da aka yi tsakanin asusun Moniepoint guda biyu.

Ita kuwa Fatima Inuwa daga jihar Kaduna, ta ce ta yi asarar Naira 40,000 a lokacin da take shirye-shiryen gudanar da bikin aurenta. Ta bayyana cewa ta ɗauki wata mai kwalliya domin gudanar da aikin kwalliyar amarya, inda matar ta buƙaci a biya ta wani kaso na kuɗin aikin tun da wuri.

Fatima ta ce ta tura kuɗin zuwa asusun Moniepoint ɗin matar, amma bayan ta karɓa sai ta daina amsa kira, ba ta kuma gudanar da aikin da aka ɗauke ta domin yi ba. Ta ce duk da kai rahoto da kuma yawan ƙorafe-ƙorafen da ta yi, har yanzu ba ta samu wani gamsasshen bayani ko mafita daga kamfanin ba. Ta bayyana cewa lamarin ya fi ba ta ciwo ne saboda kuɗin wani muhimmin ɓangare ne na shirye-shiryen bikinta.

A Abuja kuwa, wani mutum mai suna Sadiƙ ya ce ya tura Naira 22,000 ga wani mai dafa abinci da ya tallata ayyukansa a intanet. A cewarsa, bayan mutumin ya karɓi kuɗin, sai ya ƙi gudanar da aikin da suka amince da shi, sannan ya daina amsa kiran waya. Sadiƙ ya ce duk ƙoƙarin da ya yi na ganin an dawo masa da kucinsa ta hannun Moniepoint bai haifar da wani sakamako ba, domin abin da yake samu shi ne yawan bibiyar ƙorafinsa da bayanai marasa gamsarwa. Ya tambayi dalilin da ya sa binciken cinikin kuɗi tsakanin asusun kamfani guda ɗaya zai zama abu mai wahala haka.

Bayo, mazaunin jihar Legas, ya ce ya tura Naira 350,000 ga wani wakilin kwastom da ya yi alƙawarin gudanar masa da wani ciniki. Sai dai a cewarsa, bayan wakilin ya karɓi kuɗin, bai cika yarjejeniyar da suka yi ba. Bayo ya ce nan take ya kai rahoton lamarin tare da gabatar da bayanan cinikin kuɗin, amma duk da shafe watanni yana bibiyar ƙorafinsa, har yanzu ba a dawo masa da kuɗinsa ba. Ya nuna damuwarsa kan tsawon lokacin da ya kamata kwastoma ya riƙa kai ƙorafi kafin ya samu ingantaccen taimako daga kamfanin da ya ajiye kuɗinsa a hannunsa.

Shi ma Dan, daga Owerri a jihar Imo, ya yi zargin cewa ya yi asarar Naira 180,000 bayan ya tura kuɗin gaba ga wani kamfanin sufuri domin yin hayar mota. A cewarsa, kamfanin ya karɓi kuɗin amma ya gaza samar masa da motar da aka yi yarjejeniya a kai. Ya ce ƙorafe-ƙorafen da ya kai wa Moniepoint sun haifar da maimaita bayanan ƙa’idoji da alƙawuran gudanar da bincike, ba tare da samun wata mafita mai gamsarwa ba.

Idan aka haɗa kuɗaɗen da waɗannan mutane biyar suka ce sun yi asararsu, sun kai Naira 767,000, inda aka bayyana cewa dukkan kuɗaɗen an tura su ne daga wani asusun Moniepoint zuwa wani asusun Moniepoint.

Saƙonnin da Moniepoint ke aika wa kwastomomi na ƙara tayar da hankali:

Wani abin da ke ƙara harzuƙa waɗanda suka yi asarar kuɗaɗen shi ne irin saƙonnin da suke samu daga kamfanin yayin da suke neman sanin matakin da aka ɗauka kan ƙorafinsu. ɗaya daga cikin saƙonnin da Moniepoint ta aika wa wani kwastoma, mai lambar ƙorafi FSED-103366, ya ƙunshi bayanin cewa kamfanin ya fahimci damuwar da kwastoman ke ciki sakamakon aika kuɗi ga masu damfara, tare da ba da haƙurin rashin jin daɗin da lamarin ya jawo masa.

Saƙon ya kuma bayyana cewa an gudanar da aiki kan ƙorafin ta hanyar imel, inda aka buƙaci kwastoman ya duba adireshin imel ɗin da ya yi rajista da shi, ciki har da wurin da saƙonnin da ba a buƙata ke shiga (Spam ko Junk), domin samun ƙarin bayani da umarnin da aka aiko masa. Kamfanin ya sake gode masa bisa haƙuri, fahimta da haɗin gwiwar da yake bayarwa, tare da tunatar da shi lambar ƙorafinsa.

Sai dai ga kwastomomin da suka shafe makonni ko watanni suna ƙoƙarin dawo da kuɗaɗensu, irin waɗannan saƙonni ba sa kwantar musu da hankali, musamman idan ba su bayyana yadda binciken yake tafiya ba, matakan da aka ɗauka ko kuma yiwuwar dawo musu da kuɗaɗensu.

Waɗanda suka yi ƙorafin sun bayyana fargabar cewa irin wannan tsarin amsa ƙorafe-ƙorafe, cike da kalaman ƙa’idoji da yawan bibiyar lamura ba tare da samun sakamako ba, na iya gajiyar da waɗanda aka cutar har su haƙura da neman haƙƙinsu.

Matsayar Babban Bankin Nijeriya kan damfarar hada-hadar kuɗi:

Waɗannan ƙorafe-ƙorafe sun zo ne a daidai lokacin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ke ƙoƙarin ƙarfafa dokoki da matakan kare haƙƙin masu amfani da ayyukan banki da kamfanonin hada-hadar kuɗi. Daga cikin matakan akwai sabbin manufofin bankin kan hada-hadar kuɗi ta tsabar kuɗi da aka sake fasaltawa, waɗanda suka fara aiki daga ranar 1 ga Janairu, 2026, da kuma daftarin ƙa’idojin yadda za a gudanar da ƙorafe-ƙorafe kan damfarar da ake yi ta hanyar yaudarar mutum ya tura kuɗinsa da kansa zuwa asusun wani, wato Authorised Push Payment Fraud — APP Fraud. Irin wannan damfara na faruwa ne lokacin da masu laifi suka yi amfani da yaudara wajen sa mutum ya tura kuɗinsa da yardarsa zuwa asusun da suke sarrafawa.

A ƙarƙashin ƙa’idojin da aka gabatar, ana buƙatar kwastoma ya kai rahoton zargin damfara cikin sa’o’i 24, ko kuma cikin sa’o’i 72 idan akwai dalili mai ma’ana da ya hana shi kai rahoton cikin wa’adin farko.

Haka kuma, ana buƙatar cibiyoyin hada-hadar kuɗi su tabbatar da karɓar ƙorafi cikin sa’o’i 24 tare da fara gudanar da bincike. Idan damfarar ta shafi cibiyoyin hada-hadar kuɗi fiye da guda ɗaya, ana buƙatar cibiyar da aka fara kai wa ƙorafin ta sanar da sauran cibiyoyin da abin ya shafa cikin mintuna 30.

Daftarin ƙa’idojin ya kuma tanadi cewa idan bincike ya tabbatar da cewa kwastoma na da haƙƙin dawo da kuɗinsa, ya kamata a biya shi cikin sa’o’i 48. Amma idan cibiyoyin kuɗi da dama ne suka shiga lamarin, ana iya ɗaukar kwanakin aiki har 16 wajen kammala biyan kuɗin.

Haka kuma, ƙa’idojin sun buƙaci cibiyoyin hada-hadar kuɗi su samar da hanyoyin kai rahoton damfara na sa’o’i 24 a kowace rana, kafa tsarin gano alamun damfara tun da wuri, tare da wayar da kan kwastomomi game da haɗarin da ke tattare da irin waɗannan laifuffuka.

Sai dai cancantar samun kuɗin da aka yi asara a matsayin diyya na dogara ne da wasu sharuɗɗa, ciki har da kai rahoto cikin lokaci, haɗin gwiwar kwastoma wajen bincike, rashin sakacin da ya taimaka wajen faruwar damfarar da kuma rashin haɗin baki da masu laifin.

Haka kuma, ana duba ko cibiyar hada-hadar kuɗin ta gaza aiwatar da matakan da suka dace na hana damfara. Saboda haka, dawo da kuɗi ba abu ne da ke faruwa kai tsaye a kowane hali ba, domin akwai wasu yanayi da za su iya hana kwastoma samun damar karɓar kuɗinsa.

Buƙatar ƙirƙirar sashe na musamman domin binciken ƙorafe-ƙorafe:

Bisa la’akari da wannan hali, ya kamata Babban Bankin Nijeriya ya yi la’akari da kafa wani sashe na musamman da zai riƙa binciken zarge-zargen sakaci, jinkirin da ya wuce ƙa’ida da kuma rashin gamsassun amsoshi daga kamfanonin hada-hadar kuɗi ta intanet, musamman idan kwastomomi sun gamu da matsala wajen dawo da kuɗaɗen da aka tura ta hanyar damfara.

Irin wannan sashe zai iya sa ido kan yadda kamfanoni ke gudanar da ƙorafe-ƙorafe, binciken dalilan jinkiri, tabbatar da bin ƙa’idojin hukumomin sa ido da kuma samar da wata hanya mai inganci da waɗanda suka gamu da matsala za su bi domin neman ɗaukar mataki. Haka kuma, ya zama wajibi kamfanin Moniepoint ya fito ya yi ƙarin bayani kan yadda yake gudanar da ƙorafe-ƙorafen da suka shafi aika kuɗi tsakanin asusun da ke ƙarƙashin tsarinsa.

Ko da yake ba lallai ne a iya dawo da kuɗi a kowane hali ba, amma kwastomomi na da haƙƙin samun cikakken bayani, bincike mai zurfi da kuma ƙoƙari na gaskiya wajen kare muradunsu. Ya kamata a lura cewa waɗannan bayanai guda biyar zarge-zarge ne da mutanen da suka shigar da ƙorafe-ƙorafen suka gabatar, kuma ba a gudanar da wani bincike mai zaman kansa da ya tabbatar da sahihancinsu ba.

Nasarar kamfanonin fasahar kuci ta dogara da kare kwastomomi:

A ƙarshe, nasarar masana’antar fasahar hada-hadar kuɗi ta Nijeriya bai kamata a auna ta kawai da saurin da ake tura kuɗi daga wannan asusu zuwa wancan ba. Ya kamata a kuma auna ta da irin ingancin kariya da ake bai wa kwastomomi, musamman idan aka samu matsala yayin gudanar da hada-hadar kuɗi. Bai kamata kwastoma ya kai matakin gajiya wa da fid da rai kafin a ɗauki ƙorafinsa da muhimmanci ba.

By ukarofi

Leave a Reply