Raɗɗa ya ƙaddamar da yaye jami’an tsaron gandun daji a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya jagoranci bikin yaye jami’an tsaron gandun daji na ƙasa 1,008, wanda aka gudanar a dandalin jama’a, Katsina.

Bikin ya gudana ne cikin tsari inda sabbin masu gadin suka nuna horon da suka samu a gaban gwamna, manyan jami’an gwamnati, jami’an tsaro da sauran baƙi.

Masu gadin, waɗanda aka ɗauka daga al’ummomin daga kananan hukumomi 34 da ke faɗin Jihar, an horar da su ne domin su yi sintiri a dazuka, su kare al’ummomin karkara, su tattara bayanan sirri, sannan su tallafa wa sojoji da sauran jami’an tsaro.

A jawabin sa, gwamna Raɗɗa ya ce amincewar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar na ɗaukar masu gadin a watan Yunin 2026 wani mataki ne mai ƙarfi na tabbatar da tsaron dazuka da kare al’ummomin karkara.

Ya ce: “Ina godiya ga Shugaban Ƙasa bisa amincewa da buƙatarmu na ɗaukar matasa 1,000 masu ƙarfi a matsayin masu gadin daji. Za su yi aiki tare da jami’an tsaro na yau da kullum da ƙungiyoyin tsaro na al’umma.”

Gwamnan ya bayyana cewa tura masu gadin zai ƙara sa ido, ya inganta tattara bayanan sirri, sannan ya ƙara rufin tsaro a al’ummomin da ke cikin haɗari, musamman waɗanda ke kusa da dazukan da ‘yan bindiga ke amfani da su a matsayin mafaka.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da cikakken goyon baya ga dukkan shirye-shiryen tsaro, tare da haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jiha da hukumomin tsaro domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.

Gwamnan ya yi kira ga sabbin masu gadin da su yi aiki cikin gaskiya, ladabi da bin doka, su kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma, sannan ya gode wa Shugaba Tinubu, ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan tsaro da duk waɗanda suka bada gudunmawa wajen nasarar shirin.

By ukarofi

Leave a Reply