Gangamin Jos: Tinubu ya tabbatar wa ‘yan ƙasa tsaro, ya ce ana horar da jami’an gandun daji 1,000

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za a gudanar da zaɓukan 2027 cikin lumana yayin da ake nuna damuwa kan rikice-rikicen siyasa a sassan ƙasar.

Tinubu, wanda ke neman ‘yan ƙasa su sake zaɓar sa a karo na biyu a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar APC, ya bayar da wannan tabbaci ne a ranar Asabar, yayin jawabinsa a taron yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a Arewa ta Tsakiya a garin Jos na Jihar Filato, inda ya kirayi masu zaɓe da su amfani da ‘yancin da dokar ƙasa ta ba su wajen yi wa APC ruwa ƙuri’u da katinan zaɓensu (PVCs).

“Wannan shi ne makaminku ga nasara; shi ne taswirar turbarku. Ku yi amfani da shi da kyau. Ku yi amfani da shi wajen zaɓar APC,” inji shi, yana mai cewa gwamnatinsu za ta tabbatar da gudanar da zaɓukan 2027 cikin lumana.

Da yake tunatar da ziyararsa ta baya a Jihar Filato domin ganawa da waɗanda hare-hare ya rutsa da su, Shugaban ya roƙi iyalan da munanan hare-haren yankin Rukuba da ke Ƙaramar Hukumar Jos ta Arewa da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama da raunata masu yawa, da su masa afuwa kan rashin ziyartar yankunansu.

Ya tabbatar musu da cewa, za a sake gina musu ƙauyukansu domin bai wa masu gudun hijira damar komawa gidajensu. Tinubu ya bayyana cewa, mutane da dama sun rasu a sanadiyyar hare-haren Jihar Filato tun daga shekarar 2001 tare da jajenta wa iyalan waɗanda suka rasu a hare-haren da suka riƙa faruwa a baya.

Ya kuma buƙaci al’umma da su kasance masu haɗin kai a tsakaninsu ba tare da la’akari da bambance-bambancen addini, yare ko siyasa ba. “Na umarci dukkan hukumomin tsaro da su ɗauki matakin da ya dace wajen tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a Filaton.”

A cewarsa, gwamnati ta riga ta siyo kyamarorin tsaro kamar yadda aka yi alƙawari kuma ana horar da jami’an kula da gandun daji guda 1,000, yana mai tabbatar wa mazauna cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin ganin ta sauƙaƙe halin matsin da al’umma suke ciki.

Kalaman Tinubu na zuwa ne ƙasa da kwana 24 da ya umarci hukumomin tsaro su gaggauta ɗaukar matakan daƙile dabancin siyasa da wasu haramtattun ayyuka da suka saɓa wa dimukraɗiyya da wasu ɓata-gari ke yi. Ya yi gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci dukkan wani nau’i na rikici ba yayin da ake gudanar da yaƙin neman zaɓe gabanin zaɓukan 2027 a faɗin ƙasar.

By Babaji

Leave a Reply