
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Zainab Musa Kwankwaso, wadda ita ce matar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ta biyu, ta shigar da ƙorafin neman a tilasta masa sakin ta a wata Babbar Kotu da ke yankin Gudu a Babban Birnin Tarayya Abuja, kamar yadda wasu takardun kotu suka bayyana da jaridar DAILY NIGERIAN ta samo.
A wata takardar sammaci mai lamba CV/97/26, an umarci gwamnan Kanon da ya je gaban kotun a ranar 17 ga Nuwamba, 2026 domin amsa wasu tambayoyi kan al’amarin. Sannan, a bayanan da ta yi wa kotu, ta ce yanke shawarar ne sakamakon zargin rashin kulawa, soyayya da sauran ma’amalolin aure na tsawon lokaci a tsakaninsu.
Zainab, ‘yar tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma abokin tafiyar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC a zaɓen 2027, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ce, wadda aka aura wa Abba a ranar 29 ga Yulin 2006. An yi auren, wanda ya yi sanadiyyar haihuwar ‘ya’ya shida ne a lokacin da take aiki a matsayin mataimakiya ga mahaifinta.
A wasu rahotanni, an ce ta kuma yi barazanar dawo masa da sadakin da ya biya a lokacin ɗaura auren nasu, lamarin da yasa take neman khul’i, wato sakin da mace ke nema da nufin dawo da sadakin da aka biya a lokacin aurenta ko wani nau’i na biyan diyya, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoto, babu wani bayani hukumance daga ɓangaren gwamnan ko makusantansa kan al’amarin.
