Yadda Gwamnan Zamfara ya barɓi baƙuncin Uwargidan Shugaban Ƙasa a gangamin matan APC

Spread the love

Uwargidan Shugaban Ƙasar Nijeriya, Sanata Oluremi Tinubu, ta samu gagarumar tarba daga dubban mazauna Jihar Zamfara da magoya bayanta yayin ziyarar da ta kai jihar. A ranar Talata ne Gwamnatin Jihar Zamfara ta shirya babban gangamin mata na jam’iyyar APC a shiyyar Arewa maso Yamma, tare da shirin tallafa wa mata da ƙarfafa musu gwiwa. An gudanar da taron ne a harabar Cibiyar Baje Kolin Kayayyaki da ke Gusau, babban birnin jihar.

Sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya sanya wa hannu a ranar 13 ga Nuwamba, 2026, ta bayyana cewa, Uwargidan Gwamnan Zamfara, Hajiya Huriyya Dauda Lawal, ce ta jagoranci shirya taron, wanda ya samu halartar tsofaffin gwamnonin jihar, matan gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma, ministoci da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar APC. Kafin fara gangamin, Sanata Oluremi Tinubu ta gana da sarakunan gargajiya na Jihar Zamfara domin neman albarkarsu da addu’o’insu.

A jawabinta, Uwargidan Shugaban Ƙasar ta bayyana ziyarar a matsayin wata muhimmiyar alama ta nuna goyon baya, tausayi da haɗin kai da al’ummar jihar, tare da tabbatar da aniyarta ta inganta walwala da ci gaban mata, musamman waɗanda ke fuskantar matsalolin rashin tsaro, talauci da ƙarancin damar samun abin dogaro da kai. “Wannan ita ce rana mafi farin ciki a rayuwata. Ban taɓa zuwa Zamfara ba, amma na ziyarci dukkan jihohin Nijeriya 36, har da Babban Birnin Tarayya Abuja. A kullum ina fatan samun damar zuwa Zamfara, kuma yau na cika wannan burin,” inji ta.

“Tun da yanzu samun damar zuwa jihar ya zama mai sauƙi, wannan ziyara farkon al’amari ne kawai; zan sake dawowa. Shugaban Ƙasa ma zai zo.Kafin na ci gaba, ina mika ta’aziyyata gare ku baki ɗaya bisa rayukan mutanen da muka rasa. Rayukansu suna da matuƙar daraja a gare mu. Ina roƙon Allah Ya gafarta musu, Ya sanya su cikin Aljannatul Firdaus, sannan Ya ci gaba da kasancewa tare da mu,” ta ƙara da cewa.

“Yau Juma’a ce, don haka dole ne mu yi gaggawa, domin muna da tallafin da za mu raba wa mata. Wannan ita ce jam’iyya kaɗai da ke tallafa wa jama’a a lokacin kamfe, amma abin ba ya tsaya ga lokacin zaɓe kawai, domin tun daga ranar farko muka fara wannan shiri na tallafa wa al’umma. Shi ya sa ba batun siyasa kawai ba ne.

“Tun da farko ma, an karrama ni da wani sarautar gargajiya a Zamfara mai taken ‘Jagabar Matan Arewa’, wanda Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Zamfara, kuma Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Muhammad Ahmad, ya ba ni. Ina godiya ga ɗaukacin sarakunan masarautun jihar.” Ta ƙara da cewa: “Ina son Zamfara, kuma ina farin cikin kasancewa a nan. Shugaban Ƙasa ya ce na isar muku da saƙonsa cewa zai ci gaba da yi muku aiki tuƙuru. Nijeriya za ta ci gaba da samun ci gaba da wadata, idan Allah Ya yarda.”

Tun da farko, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya gode wa Sanata Oluremi Tinubu bisa irin goyon bayan da take bai wa jihar, musamman ta hanyar shirin Renewed Hope Initiative, wanda ya haɗa da shirin kai kayan abinci ga al’umma. Gwamnan ya bayyana cewa zuwan Uwargidan Shugaban Ƙasar ya wuce ziyarar aiki ta yau da kullum, yana mai cewa kasancewarta a jihar ya kafa wani sabon tarihi a tarihin Zamfara. “Uwargidan Shugaban Ƙasa, uwarmu ta ƙasa, kasancewarki a nan a yau ya wuce ziyarar aiki kawai. Kin kafa wani tarihi na musamman a tarihin jihar Zamfara mai albarka,” inji shi.

“Uwargida, da sauran manyan baki, a Jihar Zamfara mun yi amanna cewa ƙarfafa wa mata gwiwa ba nauyin gwamnati ne kawai ba, a’a, muhimmin jari ne da ya kamata a zuba domin inganta ɗabi’un al’umma, bunƙasa tattalin arziki, tabbatar da zaman lafiyar iyalai da samar da zaman lafiya mai ɗorewa.

“Ina tabbatar miki cewa Gwamnatin Zamfara da al’ummarta suna nan daram wajen goyon bayan sake zaɓen Shugaban Ƙasa a wa’adi na biyu. Da taimakon matan da ke nan da kuma mazajen da ke mara musu baya, Zamfara da dukkan jihohin Arewa maso Yamma za su tabbatar da nasarar Shugaban Ƙasa a zaɓen Janairun 2027.”

By Babaji

Leave a Reply