2027: Duk kansilan da ya tabbatar da nasarar Tinubu a mazaɓarsa zai samu tukwicin miliyan N10 – Wike

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi alƙawarin bayar da kyautar Naira miliyan 10 ga kowane kansila da ya samu nasarar kai wa Shugaba Bola Tinubu da sauran ’yan takarar jam’iyyar APC nasara a gundumarsa a babban zaɓen 2027.

Rahoton Blueprint Manhaja ya ce Wike ya yi wannan alƙawari ne ranar Litinin yayin taron masu ruwa da tsaki na ƙungiyar Rainbow Coalition a ƙaramar Hukumar Kwali, wanda sarakunan gargajiya, masu ruwa da tsaki a siyasa da mazauna yankin suka halarta.

A yayin taron, Wike ya buƙaci kansilolin da su ƙara himma wajen wayar da kan mazauna yankunansu da ƙungiyoyin al’umma domin tabbatar da nasarar APC a gundumominsu, kamar yadda Channels Television ta ruwaito.

Ya ce: “Duk kansilan da ya kai wa jam’iyya nasara a gundumarsa zai samu kyautar Naira miliyan 10. Saboda haka, ku je ku gana da shugabanninku, ku gana da ƙungiyoyin matasa da sauran ƙungiyoyi. Mu tabbatar mun kai wa Shugaban ƙasa nasara a gundumominmu.”

Ministan ya kuma bayyana goyon bayansa ga ƙoƙarin Tinubu na neman wa’adi na biyu, tare da bayyana goyon bayansa ga Sanata Philip Aduda a kujerar Sanatan FCT da Danladi Chiya a kujerar Majalisar Wakilai ta Abuja ta Kudu.

Ya ce: “Ba na buƙatar in ƙara yi muku wa’azi. Abin da kuke gani a gabanku shi ne za ku bi, ba wanda zai yi muku alƙawuran da ba zai cika ba. Zan kwanta barci a daren yau cikin kwanciyar hankali domin na san Kwali, Gwagwalada da Abaji duk suna tare da APC dari bisa ɗari.”

Ministan ya kuma zargi jam’iyyun adawa da wasu ’yan siyasa da nuna bambanci a yadda suke kallon hukuncin kotuna.

Wike ya soki ’yan adawar da suka riƙa sukar hukuncin kotuna, inda ya kawo misalin hukuncin da ya soke tikitin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Atiku Abubakar.

Yayin da yake kwatanta yadda ’yan adawa suka mayar da martani kan hukuncin kotu a lokuta daban-daban, ya ce suna kallon bangaren shari’a a matsayin mai gaskiya ne kawai idan hukuncinsa ya yi daidai da abin da suke so.

Ya ce: “Lokacin da ADC ta kai ƙara kotu kuma ta yi nasara a Kotun ƙoli, sai suka ce, ‘Kotu ita ce mafakar ƙarshe,’ ‘Kotu ta ceci dimokuraɗiyya,’ da kuma ‘Mun san bangaren shari’a ba zai ba mu kunya ba.’

“Amma da suka sha kaye a wata ƙara, sai suka fara cewa Shugaban ƙasa yana amfani da kotu wajen yaƙar ’yan adawa. Idan hukuncin ya yi maka daidai, sai ka ce bangaren shari’a yana gaskiya. Idan kuma bai yi maka daidai ba, sai ka ce ana amfani da shi wajen rusa dimokuraɗiyya. Wane irin tsari ne muke tafiyarwa?” in ji shi.

Ministan ya kuma kare matakin gwamnatinsa na samar da sabbin motocin SUV ga sarakunan gargajiya masu daraja ta farko a FCT, matakin da ya jawo suka daga wasu masu sharhi kan siyasa.

Yayin da yake watsi da zargin cewa motocin kyauta ne na siyasa ko cin hanci, Wike ya ce sarakunan gargajiya sun cancanci mutuntawa da daraja.

Ya ce: “Shin kuna son babban sarki ya riƙa tafiya a hanya da sanda a hannu, yana hawa motar haya, har wata rana mota ta buge shi? Amma kuna ganin ya dace sakataren yaɗa labaran gwamna, shugaban ƙaramar hukuma ko shugaban ƙasa ya riƙa hawa mota kirar SUV?

“Maimakon su yi amfani da matsayinsu wajen tallafa wa abubuwa masu kyau, sai masu suka suke juya lamarin ta wata fuska. Za mu samar wa sarakunanmu abin da ya dace da su, kuma babu abin da zai canza saboda ƙorafin da suke yi.”

Wike ya ce gwamnatinsa ta gudanar da ayyukan more rayuwa da dama a ƙananan garuruwan FCT, ciki har da gina hanyoyi sama da kilomita 270, inda aka aiwatar da kilomita 95 a ƙaramar Hukumar Kwali.

Ya bayyana cewa ayyukan hanyoyi da ake gudanarwa a ƙananan garuruwan FCT sun kusa kammalawa, kuma za a ƙaddamar da su a watan Disamba.

Ministan ya ƙara da cewa ƙungiyar Rainbow Coalition na aiki ne domin amfanin al’ummar FCT baki ɗaya, yana mai cewa tsarin ƙungiyar a matakin tushe yana haɗa kan jama’a daga ɓangarorin siyasa daban-daban domin inganta wakilci da ci gaba.

Ya ce: “Irin matakan da Shugaban ƙasa yake ɗauka ba irin waɗanda sauran ’yan siyasa za su iya ɗauka ba ne. Yana fitar da mu daga inuwa zuwa zahiri, kuma wannan shi ne abin da shugaba nagari ya kamata ya yi wa al’ummarsa.”

Yayin da yake kwatanta gwamnatin Tinubu da gwamnatocin baya, Wike ya lissafa kafa Hukumar Ma’aikatan Gwamnatin FCT, naɗa Shugaban Ma’aikatan FCT, bai wa ƙananan hukumomin FCT ’yancin cin gashin kai na kuɗi da kuma inganta ayyukan more rayuwa a ƙananan garuruwa a matsayin wasu daga cikin nasarorin gwamnatin yanzu.

Ya koka kan abin da ya bayyana a matsayin wariya da aka yi wa FCT a baya, yana mai cewa duk da cewa yankin na da al’umma tsakanin miliyan shida zuwa bakwai, yana da kujerar Sanata guda ɗaya da kujerun Majalisar Wakilai guda biyu kacal.

Ya ce: “Tsawon shekaru 50 babu wanda ya tuna da ku. Shugaban ƙasa ya sauya wannan yanayi, ya samar muku da ma’aikatar gwamnati taku, ya ba ku damar ɗaukar ma’aikatanku, sannan ya ɗaukaka martabar masarautunku. Ba za ku iya yin kuskure a 2027 ba.”

Ministan ya kuma yi alƙawarin duba batun albashin kansilolin FCT bayan ƙorafin da Shugaban ƙungiyar Kansiloli ta ƙasa reshen FCT, Gambo Hamza, ya gabatar.

Hamza ya bayyana cewa kansilolin yankin na karɓar albashin Naira 260,000 a kowane wata, inda ya buƙaci Wike ya shiga tsakani domin duba batun.

By ukarofi

Leave a Reply