Shugaba Tinubu ya yi alƙawarin farfaɗo da cigaban Jihar Filato da bunƙasa tattalin arziki

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Jos

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa al’ummar Jihar Filato alƙawarin samar da sabbin matakan ƙarfafa cigaban zaman lafiya da ingantaccen tsaro, tare da tabbatar da ganin an sake farfaɗo da ƙauyukan da ýan ta’adda suka tarwatsa domin mazauna yankin da yanzu ke watse suna gudun hijira su koma mahallansu cikin aminci.

Shugaban ƙasar ya bayyana haka ne a Jos yayin da jagoranci shugabannin jam’iyyar APC a matakin ƙasa da jihohi, domin gudanar da taron yaƙin neman sake zaɓen sa a shiyyar Arewa ta Tsakiya kafin babban zaɓen ranar 16 ga Janairu, 2027.

Gangamin taron ya samu halartar dubban magoya bayan jam’iyyar APC daga jihohin Arewa ta Tsakiya da kuma ƙananan hukumomin jihar Filato 17 da suka halarci taron tun da sanyin safiya, suna tsimayin isowar shugaban ƙasar.

Shugaban ƙasa Tinubu ya isa filin taron ƙarƙashin rakiyar Gwamnan Jihar Filato Gwamna Caleb Manasseh Mutfwang, Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa Sanata Abdulaziz Yari, Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da sauran shugabannin jam’iyyar APC, ministoci, ýan Majalisar Ƙasa daga Jihar Filato da maƙwaftan jihohi.

Dandazon magoya bayan da suka tarbe shi sun haɗa da membobin ƙungiyar tallafa wa Tinubu/Shettima ta A4A ƙarƙashin jagorancin tsohon Gwamnn Jihar Jigawa, Abubakar Badaru, ƙungiyoyin City Boy Movement, ƙungiyoyin mata, matasa da ‘yan kasuwa sun nuna wa Shugaban ƙasa kyakkyawar tarba, tare da rera waƙoƙi na nuna goyon baya ga Tinubu da Jam’iyyar APC.

A jawabinsa, Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya gode wa al’ummar Filato saboda juriya da haƙuri da suka nuna wajen tsimayinsa, duk da jinkirin da ya samu na rashin isar sa da wuri. Ya kuma tabbatar musu da cewa gwamnatinsa na mai da hankali wajen sake gina al’ummomin da rikice-rikicen baya suka shafa da mayar da ‘yan gudun hijira zuwa gidajensu na asali.

“Za mu yi aiki tare da ku don sake gina al’ummomin da rikice-rikice suka shafa. Mu yi aiki tare a matsayin ƙasa ɗaya al’umma ɗaya don cigaban ƙasa. Ina so ku tabbatar da katin zaɓen ku na PVC yana nan tare da ku, kuma ku tabbatar kun yi amfani da shi a matsayin makami na kawo canji, kuma a matsayin hanyar zuwa ga gaci. Za mu yi aiki tare don inganta walwalar al’ummar mu, sa yadda za mu ƙara bunƙasa tattalin arziƙinmu,” in ji Tinubu.

A game da tsaro, shugaba Tinubu ya yi alkawarin ƙarfafa ayyukan tsaro a dukkan faɗin jihar, inda ya tabbatar wa da jama’a cewa, zai yi aiki tare da gwamnan jihar don sake gina ƙauyukan da rikice-rikice suka lalata, tare da dawo da ingantaccen zaman lafiya a kowanne lungu na Jihar Filato, da Nijeriya baki ɗaya.

A cewarsa, “Muna ƙara tura jami’an tsaro da kuma ƙarfafa haɗa kai tsakanin sauran rundunonin tsaro, domin mayar da martani cikin gaggawa a duk lokacin da aka samu wani hari. Yanzu haka ana horar da ƙarin wasu jami’ai dubu ɗaya masu tsaron daji.”

A game da batun tattalin arziƙi, shugaba Tinubu ya yi alƙawarin tallafawa cigaban Filato ta hanyar samar da hanyoyi masu kyau da ingantaccen tsarin sufuri, don a iya fitar da kayayyakin noma, ciki har da shirin mayar da filin jirgin saman jihar zuwa filin jigilar kayayyaki.

A nasa jawabin, Gwamna Caleb Mutfwang ya roƙi a goyi bayan jama’ar Filato su bai wa shugaban ƙasa cikakken haɗin kai don ya sake dawowa karo na biyu, ta hanyar ba shi ƙuri’u masu rinjaye a zaɓen ranar 16 ga Janairu, 2027.

Mutfwang ya kwatanta Tinubu a matsayin abokin al’ummar Filato da yankin Arewa ta Tsakiya, inda ya ambaci sa hannun gwamnatin tarayya a harkokin samar da hanyoyi, kiwon lafiya da sauran fannoni.

Gwamnan ya kuma nemi Tinubu ya taimaka wajen kammala aikin babban filin wasan jihar wanda ya ce an fara shi kimanin shekaru 40 da suka wuce, da nufin inganta shi zuwa matakin na ƙasa da ƙasa.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, da Abdul’Azeez Yari sun yi gabatar da jawabai na neman goyon baya a wajen jama’a don sake zaɓen Tinubu da Shettima a karo na biyu.

Shettima ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta samar da kuɗaɗe har Naira biliyan 11.34 ta hanyar Kudin Tallafin Ilimi na NELFUND ga ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi a faɗin Jihar Filato.

Ya roƙi masu zaɓe da cewa, “A ranar 16 ga Janairu na shekara mai zuwa, ku tara ƙuri’un ku ga shugabanmu mai girma shugaban ƙasa. Ina so ku kaɗa ƙuri’unku ga shugabanmu. Ina so ku kaɗa ƙuri’unku ga gwamnanmu.”

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya tabbatar wa mazauna Jihar Filato cewa gwamnatin Tinubu na mayar da hankali wajen kawar da rashin tsaro da tabbatar da mayar da al’ummomin da aka raba su da gidajensu zuwa gidajensu na asali.

Daga bisani, Shugaban Jam’iyyar APC Nentawe Yilwatda ya mika tutocin jam’iyyar ga ‘yan takarar gwamna na APC a jihohin yankin Arewa ta Tsakiya.

Shugaban ƙasa Tinubu ya kuma ƙaddamar da manyan ayyukan cigaba guda uku da gwamnatin jihar ta aiwatar da suka haɗa
Cibiyar Kasuwancin Ayyukan Waje ta BPO,
Cibiyar Ayyuka ta Musamman ta P-SAC, da manyan motocin safa-safa guda 50, da za su riƙa gudanar da ayyukan sufuri a tsakanin ƙananan hukumomin jihar 17.

By ukarofi

Leave a Reply