Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a Jihar Katsina, Sanata Yakubu Lado Ɗanmarke, ya yi alƙawarin bayar da kiwon lafiya kyauta ga al’ummar Jihar idan aka zaɓe shi a matsayin Gwamna a zaɓen 2027.
Lado ya yi wannan alƙawari ne a yayin da yake ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamna mai mambobi 2,000 a sakatariyar jam’iyyar ta jiha da ke Katsina.
Ya ce gwamnatinsa za ta ba da fifiko ga kiwon lafiya kyauta ga dukkan mazauna jihar, da ilimi da inganta tsaro, waɗanda ya bayyana a matsayin muhimman fannoni da suka ja baya a ƙarƙashin gwamnatin yanzu.
Tsohon Sanatan ya tabbatar wa mazauna jihar cewa samun magani ba zai sake dogara da ƙarfin kuɗin mutum ba, yana mai alƙawarin cewa marasa lafiya za su samu magani a asibitoci ba tare da biyan ko sisi ba.
Ya ce: “Ba zan bari duk wanda ba shi da lafiya ya biya ko sisi a asibiti ba idan aka zaɓe ni a matsayin gwamna a 2027.”
Lado ya kuma soki aikin gwamnatin yanzu, yana mai zargin cewa Jihar Katsina ta samu ƙarancin ci gaban ɗan adam a cikin shekaru uku da suka gabata.
Ya nuna damuwa kan abin da ya bayyana a matsayin faɗuwar matsayin ɓangaren ilimi da ci gaban matasa, yayin da yake zargin gwamnati da gazawa wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar al’ummomi a faɗin jihar.
A cewar Lado: “A cikin shekaru uku da suka gabata, ilimi ya ja baya a Jihar Katsina. Rashin tsaro ma wata damuwa ce da ke addabar jihar, wadda muka shiga ciki sakamakon rashin gudanarwa mai kyau a cikin shekaru uku da suka gabata.”
Tsohon Sanatan daga Shiyyar Funtua ya tabbatar wa magoya bayan jam’iyya cewa gwamnatinsa za ta bi wata hanya daban ta ci gaba idan aka zaɓe shi, yana mai alƙawarin yin aiki tare da tawagarsa domin inganta arziƙin jihar. Ya ce: “Za mu canza labari idan aka ba mu dama. Tare da tawaga ta, Insha Allah, Katsina za ta zama jiha abin koyi a tarayya.”
Tun da farko, Shugaban PDP na Jiha, Nura Amadi Kurfi, ya ce kafa kwamitin yaƙin neman zaɓe mai mambobi 2,000 ya nuna ƙudurin jam’iyyar na samun nasara a zaɓen gwamna na 2027. Ya bayyana ƙwarin gwiwa kan ƙwarewa da bambancin mambobin kwamitin, yana mai cewa sun haɗa da ‘yan kasuwa, ma’aikatan gwamnati masu ritaya, tsofaffin jami’an tsaro, ɗalibai da mata, da sauransu.
Kurfi ya yi kira ga mambobin kwamitocin daban-daban da su nuna jajircewa, su ƙarfafa wayar da kan jama’a a matakin ƙasa, su kuma yi aiki tare domin cimma burin zaɓe na jam’iyyar. An kuma naɗa Janar mai ritaya, Sagir Musa, a matsayin Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen gwamna na PDP domin samun nasara.
