JAMB na shirin daƙile haɗin-gambiza wajen zaɓar darussa, ta samar da manhajar gabanin rajista

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu JAMB, ta ce ta shirya gabatar da wasu gyare-gyaren fasaha gabanin jarrabawar UTME, ciki har da samar da manhajar kafin rajista, tsaurara matakan tantancewar kwamfuta, da tsarin da zai hana ɗalibai aikata kurakurai wajen zaɓar darussa.

Waɗannan gyare-gyare na da nufin rage wahalhalun da ɗalibai ke sha wajen rajista, hana satar amsa da ƙarfafa wa lamuran tsayar da gaskiya da adalci wajen neman gurbin karatu. Haka kuma zai bai wa ɗalibai damar samun labarai akan gurbin karatu gabanin su zaɓi kwasa-kwasan da za su yi karanta da kuma makarantar da suke so.

Rajistaran JAMB, Farfesa Segun Aina ne ya bayyana haka a ranar Asabar a Abuja, inda ya ƙara da cewa sabon tsarin zai bai wa ɗalibai damar yin rajista daga gida kafin su garzaya zuwa cibiyoyin da ta amince da su don kammala rajista. Farfesan ya yi wannan jawabi ne bayan tattakin motsa jiki na tsawon kilomita biyar da ma’aikatan hukumar suka shirya a matsayin ɓangare na shirye-shiryen jarrabawar UTME ta 2027.

Ya bayyana cewa, manhajar da ake shirin samarwa za ta taimaka wa ɗalibai samun bayanansu daga Hukumar kula da Lamuran Shaidar Zama Ɗan Ƙasa (NIMC), shigar da bayanansu da kuma zaɓar darussan da suke so, fannonin karatu da makarantu gabanin ainihin rajistar, yana mai ƙarawa da cewa manhajar za ta taimaka musu wajen samun bayanai da dama ciki har da makin shiga na shekarar da ta gabata ga kwasa-kwasan da suke so.

By Babaji

Leave a Reply