
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin cigaba da gudanar da aikin haƙo mai a filin mai na yankin Kolmani muddin ‘yan Nijeriya suka zaɓe shi a zaɓukan 2027.
Atiku Abubakar ya bayyana haka ne a ranar Asabar, yayin yaƙin neman zaɓen ADC a Jihar Bauchi, inda ya kuma yi alƙawarin dawo da tallafin fetur da na lantarki, ƙarfafa lamuran tsaro a Arewa maso Gabas da dawo da aikin samar da tashar lantarki ta Mambilla a Jihar Taraba.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma bayyana ƙwarin-gwiwarsa ga al’ummar Bauchi, inda ya yi kira a gare su da kasancewa masu jajircewa wajen kare ƙuri’unsu da tabbatar da cewa adalci ya yi nasara a baki lamuran zaɓen na 2027. Haka kuma, ya roƙi masu zaɓe da su zaɓe ‘yan takarar ADC a kowane mataki a zaɓukan da ke tafe.
Shugaban jam’iyyar na Ƙasa, Sanata David Mark, wanda ya samu wakilcin Sakataren jam’iyyar na ƙasa, Rauf Aregbesola, ya bayyana gamsuwa da dandazon jama’ar da suka halarci gangamin, yana mai cewa hakan ya nuna yadda ADC ta samu karɓuwa a Jihar Bauchi, wadda tuni ta shirya goyon bayan jam’iyyar.
Ya yi kira ga magoya baya da kada su biye wa ‘yan adawa kan ayyukan za su fusata su, a madadin haka su mayar da hankali wajen tara wa ADC jama’a domin samun ruwan ƙuri’u a zaɓukan.
Darakta-Janar na yaƙin neman zaɓen jam’iyyar, Sanata Augustine Akobundu, ya yi wa Gwamna Bala Mohammed godiya bisa bai wa ADC damar aiki da kayayyakin gwamnati yayin taron, inda ya kirayi sauran gwamnoni da su samar da yanayi mai kyau ga harkokin siyasa ba tare da la’akari da bambance-bambancen siyasa ba.
