Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
Shugaban ƙungiyar ’Yan Kasuwar Singa da suka yi gobara, waɗanda ke fafutukar ganin an biya su tallafin gobarar kasuwar Sabon Gari da Gwamnatin Kano ta yi alwashin bayarwa ta hannun Gwamna Abba Kabir Yusuf bayan faruwar lamarin, Alhaji Kabiru Adamu Gano, ya bayyana cewa har yanzu ’yan kasuwar ba su samu tallafin ba.
Ya ce, duk da cewa Gwamna Abba ya bayyana a wani jawabi cewa kuɗin tallafin naira biliyan 8 suna hannunsa, har yanzu ’yan kasuwar ba su karɓi kuɗin ba, kamar yadda ya bayyana wa manema labarai.
Haka kuma, ya ce a ƙoƙarin da suke yi na ganin an biya su tallafin, sun samu zama da gwamnan har a Abuja, amma har yanzu ba a cimma matsaya ba.
Ya bayyana cewa ’yan kasuwar da suka yi asara sakamakon gobarar suna matsa musu lamba, har sun rasa abin da za su gaya musu. Ya ce da farko suna ƙoƙarin kwantar musu da hankali, amma yanzu ma wasu sun daina yarda da bayanan da suke ba su a matsayinsu na wakilansu.
Ya ce abin takaici ne yadda suka ji an biya takwarorinsu na Kudu tallafi mai yawa cikin ’yan kwanaki kaɗan bayan faruwar gobarar.
Saboda haka, sun roƙi Gwamna Abba, bisa tausayi da adalci, da ya biya su tallafin Gwamnatin Tarayya da kuma wanda gwamnoni suka haɗa, wanda jimillarsa ta kai naira biliyan 8.
Haka shi ma Bature Ali, shugaban ƙungiyar Gidan Gashash, ya ce rashin jari ya jefa su cikin mawuyacin hali, inda suke neman tallafi daga Gwamnatin Kano a wannan lokaci da suke fuskantar matsaloli ta fuskar kasuwanci da rayuwar yau da kullum.
