Rasha da Ukraine sun sake komawa teburin sulhu

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Bayan shafe shekaru ana gwabza yaƙi wanda ya jawo asarar rayuka, lalacewar muhimman ababen more rayuwa da kuma raba iyalai da muhallansu, Rasha da Ukraine sun sake samun damar tattaunawa kai tsaye a wani sabon yunƙuri na neman kawo ƙarshen rikicin da ke tsakaninsu.

Rahoton kamfanin dillancin labarai na Reuters, ya bayyana cewa wakilan ƙasashen biyu sun gana a birnin Abu Dhabi na ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa, a wani taron sulhu da Amurka ke jagoranta.

Wannan shi ne karon farko da wakilan ƙasashen biyu suka gudanar da irin wannan tattaunawa tun bayan watan Fabrairun shekarar 2026.

Taron ya samu halartar wakilan Amurka, ciki har da Jared Kushner da Steve Witkoff, yayin da ɓangaren Rasha da Ukraine suka tura wakilan da ke jagorantar tawagoginsu.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, ya bayyana tattaunawar a matsayin mai amfani, yayin da shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya bayyana cewa an tattauna muhimman batutuwa.

Daga cikin batutuwan da suka fi ɗaukar hankali akwai yiwuwar musayar fursunonin yaƙi, dawo da fararen hula da yara da aka tsare, da kuma samar da tabbacin tsaro ga Ukraine.

Sai dai duk da wannan sabon yunƙuri na sulhu, akwai manyan batutuwan da har yanzu ke raba ƙasashen biyu.

Rasha na son Ukraine ta amince da wasu sauye-sauye da suka shafi yankunan da ake takaddama a kansu, tare da yin watsi da burinta na shiga ƙungiyar tsaro ta NATO.

A nata ɓangaren, Ukraine ba ta amince da miƙa yankunanta ba, tana kuma neman a samar da ingantaccen tsarin tsaro kafin cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

By ukarofi

Leave a Reply