Gidauniyar Mangal ta ƙaddamar da tiyatar Fibroid, Appendix kyauta a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gidauniyar Alhaji Ɗahiru Bara’u Mangal ta ƙaddamar da shirin yi wa mutane 2,800 masu fama da cututtukan mahaifa (Fibroid) da makero (Appendicitis), da sauran cututtuka tiyata kyauta a Jihar Katsina.Shirin na daga cikin faɗada ayyukan tallafin kiwon lafiya na gidauniyar, wanda ya ƙunshi ba da magunguna, duba lafiya da gudanar da tiyata kyauta ga marasa galihu.

A yayin ƙaddamar da shirin na zangon ƙarshe na shekarar 2026 a ranar Asabar a Katsina, Alhaji Hussaini Kabir, mamba a kwamitin amintattu na gidauniyar, ya ce sama da mutane 7,000 sun amfana da ayyukan kiwon lafiyarta a faɗin jihar a shekarar.Ya bayyana cewa wannan shi ne karo na uku da gidauniyar ta gudanar da shirin tallafin kiwon lafiya a shekarar 2026, inda ake sa ran sama da marasa lafiya 800 za su amfana da wannan zangon.Kabir ya ce an faɗada shirin ne domin bai wa masu ƙaramin ƙarfi da marasa galihu damar samun kulawar lafiya, musamman waɗanda ba su da ƙarfin biyan kuɗin magani ko tiyata.Ya bayyana cewa cututtukan da shirin ya ƙunsa sun haɗa da Fibroid, Appendicitis, hernia da hydrocele, da sauran matsalolin lafiya da ke buƙatar kulawar ƙwararrun likitoci.

A cewarsa, ana tantance dukkan marasa lafiyar da suka zo domin gano irin matsalolin da suke fama da su, tare da tantance waɗanda ke buƙatar tiyata ko wasu nau’ikan magunguna.Ya ce waɗanda aka gano suna buƙatar tiyata za a yi musu aikin kyauta, yayin da sauran za su samu magunguna da shawarwarin ƙwararrun likitoci ba tare da biyan komai ba.Kabir ya jaddada cewa gidauniyar ba ta ƙayyade adadin mutanen da za ta tantance ba, inda ya ce duk wanda ya zo neman kulawar lafiya za a duba shi.Ya ƙara da cewa shirin a buɗe yake ga dukkan ‘yan Najeriya ba tare da la’akari da jiha ko asalin mutum ba, kuma babu wani mai amfana da za a caza kuɗin hidimar.Ya ce shugaban gidauniyar, Alhaji Ɗahiru Bara’u Mangal, ne ke ɗaukar nauyin shirin gaba ɗaya, a matsayin gudummawarsa wajen tallafa wa marasa galihu a cikin al’umma.

Dangane da kula da lafiyar ido, Kabir ya ce gidauniyar ta kuma samar da duba idanu kyauta, tiyatar ido, tabarau da magunguna ga mutanen da ke fama da matsalolin gani.Ya bayyana cewa an tsara wannan bangare ne domin taimaka wa wadanda ke fama da matsalar gani amma ba su da ƙarfin biyan kuɗin magani ko sayen tabarau.Kabir ya bayyana cewa tun bayan kafa gidauniyar a shekarar 2018, ta tallafa wa mutane sama da 33,507 ta hanyar shirye-shiryen jin ƙai daban-daban.Ya ce a shekarar 2026 kaɗai, kimanin mutane 10,200 ne suka amfana da ayyukan kiwon lafiya kyauta kan cututtuka da matsalolin lafiya daban-daban.Ya kara da cewa ayyukan gidauniyar sun hada da tallafin ilimi da sauran ayyukan jin kai domin inganta rayuwar marasa galihu.Kabir ya yaba wa Gwamnatin Jihar Katsina bisa goyon bayan da take bai wa gidauniyar, musamman ta fuskar samar da cibiyoyin kiwon lafiya da ma’aikatan lafiya domin inganta ayyukan shirin.Shi ma Dakta Aliyu Ibrahim Zakka, daya daga cikin likitocin da ke gudanar da aikin, ya yi karin bayani kan yadda ake tantance marasa lafiya da gano wadanda ke bukatar tiyata.

Daya daga cikin wadanda suka amfana, Rabi’atu Ibrahim, ta nuna godiyarta ga gidauniyar, tana mai cewa tallafin ya kawo mata sauki.Haka kuma, Malama Hafsat Adamu ta yaba wa shirin, tare da kira ga masu hannu da shuni da su yi koyi da Alhaji Mangal wajen tallafa wa marasa galihu.Waɗanda suka amfana sun yi addu’ar Allah ya ƙara wa Alhaji Mangal da iyalansa lafiya da arziki, tare da roƙon ya ci gaba da gudanar da ayyukan jin ƙai.An fara gudanar da wannan shirin ne a babban asibitin Katsina, da kuma asibitin idanu, a matsayin wani ɓangare na ayyukan tallafin kiwon lafiya da gidauniyar ke gudanarwa lokaci zuwa lokaci.

By ukarofi

Leave a Reply