An buƙaci gwamnatin Katsina ta dawo da tsofaffin ƙofofin birnin domin kiyaye tarihi da al’adu

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wani mai kishin tarihi da al’adun al’ummar Katsina, Abdullahi Muhammad Katsina, ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta yi la’akari da dawo da wasu daga cikin tsoffin ƙofofin birnin Katsina da suka haɗa da Ƙofar Ƙwaya, da Ƙofar Ƙaura, da Ƙofar Yanɗaka da Ƙofar Sauri, domin kiyaye tarihi da al’adun gargajiyar jihar.

Abdullahi Muhammad ya bayyana cewa, dawo da waɗannan kofofi zai taimaka wajen adana muhimman abubuwan tarihi da suka shafi asalin birnin Katsina, tare da bai wa al’ummomin da za su zo nan gaba damar ganin wadannan wurare da idonsu, maimakon su rika jin sunayensu kawai ta hanyar labarai.

A cewarsa, bai kamata a bar waɗannan muhimman wuraren tarihi su kasance cikin abubuwan da ake tunawa da su kawai ba, alhali akwai damar sake farfado da su domin amfanin al’umma da kuma ilmantar da masu tasowa.

Rasa wadannan kofofi ya biyo bayan ayyukan faɗada hanyoyin cikin birnin Katsina da Gwamnatin Jihar Katsina ta gudanar, lamarin da ya sa yake ganin ya dace a duba hanyoyin da za a bi wajen dawo da su ko kuma sake gina su bisa tsarin da zai kiyaye sahihancin tarihinsu.

Wannan kira ya sake jawo hankali kan muhimmancin da ke tattare da kare kayayyakin tarihi da wuraren gargajiya, musamman a birnin Katsina mai ɗimbin tarihi da al’adu.

Kiyaye tarihi shi ne girmama asalinmu, domin al’ummar da ta san tarihinta, tana da damar fahimtar inda ta fito da kuma abin da ya kamata ta bar wa masu zuwa bayanta a cewar Abdullahi.

By ukarofi

Leave a Reply