Yadda APC za ta iya ci gaba da mulki har shekara 32

Daga IBRAHIM SHEME

A ranar Talata, shugaban riƙo na jam’iyyar APC na ƙasa, Mai Mala Buni, ya faɗi wata magana wadda ta bar baya da ƙura. A cewar sa, jam’iyyar za ta ci gaba da mulkin Nijeriya har zuwa shekaru 32 masu zuwa; wato dai, har zuwa shekara ta 2053. Idan ka haɗa da shekaru shida da ta yi daga 2015 zuwa yau, za ka samu shekara 38 kenan.

Na so a ce Mai Mala Buni ya faɗa mana kuma yadda mulkin jam’iyyar zai ƙare a cikin 2053 tunda dai a nan ya yi mata iyaka. Shin a lokacin ne za su yarda a kayar da su a zave ko kuma su ne za su ce sun gaji da mulkin? Tun a nan, ban ga basirar yanke hukuncin shekaru nawa jam’iyyar za ta yi ta na mulki ba.

Sai dai da alama ’yan APC sun yi murna da jin wannan magana ta Buni. Masu fargabar faxuwa a zaven da za a yi a 2023 sun qara gyara zama tare da ajiyar zuciya. Sun ce, “Ashe dai manya su na yi mana babban shiri, miyar mu za ta ci gaba da yin ja.”

Shin wane babban shiri ne wannan? Mai Mala Buni, wanda shi ne gwamnan Jihar Yobe, ya ɗan vuntuna mana sirrin. Lokacin da ya yi maganar dai ya yi ta ne a wajen ƙaddamar da wani kwamitin tuntuɓa da dabarun cin zaɓe wanda jam’iyyar ta kafa, a sakatariyar ta da ke Abuja.

A cewar sa, an kafa kwamitin na mutum 61 ne domin a tabbatar da ɗorewar jam’iyyar ta hanyar ƙarfafa ta. Kwamitin zai gano hanyoyin da za a bi a tabbatar da cewa ƙarfin jam’iyyar ya ƙaru, musamman yanzu da aka fara sunsunar babban zaɓen da ke tafe.

Ya ce, “An kafa kwamitin dabaru da tuntuva ne domin a ɗora a kan nasarorin da mu ke samu wajen gina jam’iyyar ta yi ƙarfi, wadda ke da kyakkyawan tsari wanda zai sanya APC ta jure duk wata wahala. Burin mu shi ne mu samar da tayar da za a tuqa jam’iyyar mu ta zarce wa’adin mulki na 6 da na 7 da na 8 domin tabbatar da aiwatar da manufofin ta, da inganta rayuwar ’yan Nijeriya, kuma ta ci gaba da zama babbar jam’iyyar Nijeriya.

Saboda haka wannan kwamiti ya na da matuqar muhimmanci wajen ganin mun cimma nasarar yin manyan tarurrukan mu na qasa kuma mu kafa jam’iyya qarfaffa wadda mutane su ka yarda da ita.” Shugaban kwamitin dai shi ne Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Badaru Abubakar.

Ba shakka, duk kowace jam’iyyar da ke mulkin ƙasa za ta so ta cimma irin wannan babban burin. Saboda haka, babu laifi idan shugabannin APC su ka tashi tsaye don ganin ba su faxi a zave ba. Ba kan su farau ba; su ma sun yi kaye ne a 2015 har su ka karɓe ragamar daga hannun PDP.

Sai dai kada mu manta, ita ma PDP ta taɓa bayyana irin wannan burin na ci gaba da mulki a zamanin ta. Hasali ma dai, a cikin 2008 shugaban PDP na ƙasa, Cif Vincent Ogbulafor, ya furta cewa PDP za ta yi mulkin shekara 60. A gaba na ya yi maganar. Mu na zaune tare a teburin manyan baƙi lokacin da aka ƙaddamar da littafin tarihin Alhaji Abdulƙadir Balarabe Musa ne a wani dare a otal ɗin Transcorp ya yi maganar. A lokacin ina Editan jaridar Leadership. Shi ya sa Leadership kaɗai ce jaridar da ta bada labarin washegari; bayan kwana ɗaya da buga labarin, sauran jaridu su ka ɗauka.

Me ya sa PDP ta kasa cimma burin ta? Ai cikin shekaru bakwai da yin maganar, ta faɗo daga kujerar mulki, APC ta qwace. A lokacin da Ogbulafor ya yi maganar cika bakin nan kuwa, gani ya ke da wuya ne PDP ta faɗi a zave. A lokacin har kiran ta ake yi jam’iyyar da ta fi kowace girma a Afrika, ganin yawan membobin ta. A cewar sa, akwai zaman lumana a cikin jam’iyyar, sannan ta ciwo wasu jihohi huxu waɗanda ba nata ba, wato Abiya, Imo, Bauchi da Sokoto; uwa-uba kuma ta na da gwamnoni 28 da ‘yan Majalisar Tarayya birjik.

To ya aka yi kuma ta faɗo ƙasa kamar ruɓaɓɓen mangwaro? Kuskure ɗaya rak: ficewar da wasu gwamnoni su ka yi daga PDP lokacin da Shugaba Jonathan ya ƙi bin buqatar su har ya yi katsalandan cikin Ƙungiyar Gwamnoni ta Nijeriya (NGF). Gwamnonin da su ka fara ficewa su ne Rotimi Amaechi (Ribas), Bukola Saraki (Kwara) da Aliyu Wamakko (Sokoto). Daga nan wasu su ka bi sahu. Kuma ga irin baƙin jinin da jam’iyyar ke da shi a wajen jama’a; to yaya lafiyar giwa ballantana ta yi hauka? Da ma tuni jirgin Baba Buhari ya na tsaye a gaɓa, don haka sai kowa ya shiga, aka bar PDP a tasha.

Ibtila’in da ya faru ga PDP ne APC ke tsoron ya faru a gare ta, ga shi ana haramar fara tafiyar 2023. To amma fa irin kuskuren da PDP ta tafka, ita ma APC ta riga ta tafka shi. Akwai mutanen da aka ware, ba a yi da su, bayan kuwa da bazar su aka yi rawa a baya. Na biyu, yanzu ita ma APC ta na da baƙin jini ko dai bai kai kwatankwacin na PDP saboda gwamnati ta gaza wajen magance matsalar tsaro, ga kuma fatara da yunwa da hauhawar farashin kayan masarufi, sannan yaƙi da cin hanci da rashawa ma ana yin sa ba kamar yadda talaka ya zaci za a yi shi ba kafin 2015.

Babbar madogarar APC dai ita ce mutuncin da aka ɗauki Shugaba Buhari da shi har aka ci zaven 2015. To, yanzu an rage masa irin wancan kallon saboda mawuyacin halin da ake ciki. Don haka akwai tsoron cewa idan babu Buhari, to babu APC.

Wani ƙusa a APC, Farfasa Tahir Mamman, wanda shi ne shugaban Kwamitin Gyaran Tsarin Mulkin jam’iyyar, ya bayyana cewa Buhari da kan sa ya na fargabar abin da zai iya faruwa ga jam’iyyar musamman daga 2023. Sai dai Farfesan ya ce ko bayan babu Buhari, jam’iyyar za ta ci gaba da mulki “tsawon lokaci.’’ Ya faɗi haka ne a taron jam’iyyar na yankin Arewa-maso-gabas wanda aka yi a Gombe shekaranjiya.

A gani na, idan har APC na so ta ɗore da mulki, to sai ta cika wa jama’a alƙawuran da ta yi masu na tabbatar da tsaro a ƙasar nan tare da magance matsalar tattalin arziki wadda ta jefa mutane cikin halin ni-’ya-su, sannan mutane su ga cewa ana aiwatar da yaƙi da cin hanci bisa adalci. Dubi abin da Gwamna Wike na Jihar Ribas ya ce, wato yaƙi da cin hanci ana yin sa ne kawai a kan ‘yan adawa.

Ya ce, “A yau, idan ina so in bar PDP in koma APC, ba za a ce ni ɓarawo ba ne. Amma da zarar na ci gaba da zama a PDP, to ni varawo ne kenan. Saboda haka batun waye varawo ya dogara ne da jam’iyyar da ka ke. Wannan shi ne yadda su ka fassara ma’anar cin hanci da rashawa.”

Irin wannan kallon da ake wa su Mai Mala Buni ne ya kamata su sauya idan har su na so su cimma burin yin mulki har nan da shekara 32. Idan ba haka ba kuwa, ba za a san maci tuwo ba sai miya ta ƙare. Mun dai sani, a 2023 babu jirgin Baba Buhari, sai dai kowa tasa ta fisshe shi.