Ƙara taɓarɓarewar harkar ilimi a Arewa

Wani rahoton musamman da jaridar Blueprint ta buga a ranar Talata ta makon jiya ya nuna cewa a cikin watanni uku kacal ’yan bindiga sun ci gaba da kai hare-hare a makarantu aƙalla guda biyar a yankunan Arewa-maso-yamma da Arewa-maso-gabas. Hakan ya haifar da damuwa a kan batun samar da ilimi ba kawai a waɗannan yankunan kaɗai ba har ma da lardin Arewa baki ɗayan sa.

Rahoton ya ambaci jihohin Katsina, Zamfara da Kaduna a Arewa-maso-yamma da kuma Neja a Arewa-ta-tsakiya a matsayin inda ayyukan ta’addancin ’yan bindigar ya fi ta’azzara. Hari na baya-bayan nan da aka kai, an kai shi ne a Makarantar Firamare ta Rema da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari da ke Jihar Kaduna, inda ’yan bindiga su ka ɗauke malamai uku amma ba su kama ɗalibi ko xaya ba. Kafin wannan, ’yan bindiga sun kai hari a Kwalejin Koyon Aikin Daji ta Tarayya (Federal College of Forestry Mechanisation) da ke Afaka, a dai wannan jihar, su ka sace ɗalibai 39 (maza 23 da kuma mata).

Amma yunƙurin ’yan bindiga na su sace ɗaliban Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati (GSSS) da ke Ikara bai cimma nasara ba saboda jami’an tsaro da ’yan sa kai sun tarwatsa su ta hanyar fin ƙarfin su da manyan makamai lokacin da su ka yi artabu da ‘yan ta’addan.

Ban da waɗannan hare-haren, ’yan bindiga sun kuma kai hari a gidajen ma’aikata na Hukumar Filayen Jiragen Sama ta Tarayyar Nijeriya (FAAN) a Kaduna, su ka sace manyan ma’aikata da iyalan su. Amma ba su samu nasara ba a yunƙurin da su ka yi na sake kai hari a gidajen, aka ce jami’an tsaro sun raunatu su sosai.

A Jihar Zamfara, ’yan ta’adda sun kai mamaya a Makarantar Sakandaren ’Yanmata ta Gwamnati (GGSS) da ke Jangebe a Ƙaramar Hukumar Talata Marafa, su ka yi awon gaba da ɗalibai 279 waɗanda bayan ’yan kwanaki aka sako su. A ranar 17 ga Fabrairu kuma, ’yan bindiga sun kutsa kai zuwa cikin Makarantar Sakandaren Gwamnati (GSS) da ke Kagara a Jihar Neja, su ka kashe ɗalibi ɗaya sannan su ka sace guda 27, har ma da wasu malaman makarantar da iyalan su. Sai da aka yi mako ɗaya kafin su sako su bayan Sheikh Ahmad Gumi da ya yi ƙoƙarin sulhu tsakanin ’yan bindigar da gwamnatin jihar ya sanya hannu a maganar.

A jihar da Shugaba Muhammadu Buhari ya fito ma, wato Katsina, ‘yan bindiga sun kai hari a Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Gwamnati (GSSS) da ke Ƙanƙara, su ka sace ɗalibai 344 a ranar 11 ga Disamba, 2020. Wannan abu ya faru awoyi kaɗan bayan Shugaban Ƙasar ya sauka a gida Daura domin yin hutun mako ɗaya. Ba a sako ɗaliban ba sai da aka kwashe kwana shida su na tsare.

A lissafi, an sace jimillar ɗalibai da malamai 692, ciki har da malamai uku da aka sace a harin da aka kai a Birnin Gwari ranar Litinin ta sama, a cikin ƙasa da watanni uku, kuma ba a sako 42 ba.
A game da harin da aka kai Birnin Gwari ranar Litinin, Kwamishin Tsaron Cikin Gida da Al’amuran Yau Da Kullum, Mista Samuel Aruwan, ya ce da farko yara biyu ne su ka vace a lokacin harin, amma daga baya an gan su. Ya ce sojoji na can su na bin sawun ’yan bindigar domin a karvo malaman.

A rahoton da Blueprint ɗin ta buga, wanda cikakke ne, an tattauna da masana kan abin da waɗannan hare-haren za su iya jawo wa harkar ilimi a Arewa. Wata malama kuma shugabar Sashen Nazarin Haɗa Magunguna a Jami’ar Jihar Kogi, Dakta Sarah Jumai Shaibu, ta ce ƙaruwar hare-haren zai janyo yawaitar yaran da ba su zuwa makaranta a yankin.

Ta ce, “Yawan yaran da ba su zuwa makaranta zai ci gaba da ƙaruwa domin iyayen da ’ya’yan su su ka kuɓuta daga hannun ‘yan bindiga za su fara wani tunani kuma ba za su so su koma makaranta ba. Daga nan sai ‘ya’yan su koma su na gararamba a titina, a nan gaba kuma waɗannan yaran ne za a ja zuwa cikin ayyukan aikata laifi.”

Manajan Gangamin Jama’a a wata ƙungiya mai zaman kan ta, wato ActionAid Nigeria, Mista Adewale Adeduntan, ya bayyana damuwa kan yawaitar sace ɗalibai da ake yi a Arewa, ya ce matsalar ta maida hannun agogo baya a Yekuwar ’Yancin Ɗan’adam ta Duniya (Universal Declaration of Human Rights) wanda ya ce: “Kowa na da haqqin a ilmantar da shi.”

Ya ce: “Abin baqin ciki ne a ce duk da matsalar da Arewa ke fuskanta kuma a dakusar da batun bada ilimi wanda muhimmain abu ne wajen kawo cigaba ta fuskar zamantakewa da tattalin arziki a yankin da kuma yadda za ta shiga a dama da ita a hadahadar tattalin arziki ta duniya.” Adeduntan ya bayyana haƙƙin samun ilimi a matsayin haqqin ɗan’adam wanda doka ta ba kowa ba tare da nuna wariyar matsayi ba, ko ga yara ko matasa ko manya.

Shi ma Manajan Shirye-shirye na Yiaga Africa, Mista Paul James, ya nuna matuƙar damuwa kan yadda yawaitar hare-hare a kan ɗaliban da ba su san hawa ba ba su san sauka ba ya ke ƙara fallasa gazawar gwamnati wajen samar da tsaron rayuwa da kuma kayayyaki. Ya ce harin da aka kai a Kaduna na kwana-kwanan nan ya ma fi zama abin damuwa domin ya faru ne duk da yawaitar hukumomin tsaro da ke akwai a Jihar Kaduna.

A gaskiya, abin takaici ne a ce a yayin da Arewa ke fama da matsalar yaran da ba su zuwa makaranta su sama da miliyan 10.5 (kimanin kashi 60 cikin ɗari na irin waxannan yaran su miliyan 13 a ƙasar nan), sai kuma ga shi matsalar na ƙara dagulewa saboda ayyukan ta’addancin da ke faruwa na Boko Haram, ‘yan bindiga da kuma sace mutane da ake ta yi, musamman a makarantu.

Idan an yi la’akari da cewa ilimi shi ne ginshiƙin gina kowace al’umma, mu na kira ga gwamnatoci a kowane mataki da su fito da hanyoyi mafi dacewa da za a magance wannan babbar matsala da ’yan ta’adda ke jawowa don wargaza ƙoƙarin da gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kan su ke yi don su haɓaka harkar ilimi a Arewa, yankin da aka ce nan ne inda ya fi ko’ina taɓarɓarewar harkar ilimi a duk duniya.

A gaskiya bai kamata ’yan Arewa da ma ’yan Nijeriya baki ɗaya su bari batun ilimi ya ƙara taɓarɓarewa ba idan har su na so su shiga da’irar al’ummomin da su ka ci gaba ta fuskar kimiyya da ƙere-ƙere a duniya.