Gudunmawar harshe da al’ada ga bunƙasa tattalin arziƙi da zaman lafiya (3)

Daga FARFESA SALISU AHMAD YAKASAI

Mafi kyawun fahimta ita ce abu ya zama da harshen mutum ake yinsa, idan ba haka ba to wasu abubuwa za su shige duhu. Tun kafin zuwan Turawa, a ƙasar Hausa ana amfani da shari’ar Musulunci ne. Wannan tsari na sharia a cikin Larabci yake, wanda ba kowa da kowa ya iya fahimta ba. Don haka da wuya jama’a su san kanta sosai da sosai, musamman ma idan wata matsala ta taso. Da Bature ya zo, shi ma dai ba ta sake zani ba. Ita tasa shariar a cikin Turanci take, ko haifaffen harshen ma sai ya yi famar fahimta tasa, balle kuma ɗan koyo. Duk a waɗannan halaye guda biyu, da wuya mutane da yawa su fahimci nau’in shari’un domin ba a cikin harshensu suke ba, ga shi da wuya koyon baƙon harshe. Babu shakka ilimi babban jigo ne a rayuwar mutum da al’umma gaba ɗaya.

Hasali ma, ai ilimi wata hanya ce wadda mutum yake amfani da ita ya gane abubuwa, ya fahimce su ta yadda zai bunƙasa sulukinsa a rayuwa (Gusau, 2010). Wani mutum, ilimi yakan daidaita tunaninsa ya zama mai tsiwurwurin rayuwa nau’i biyu, wato rayuwa ta duniya da kuma ta lahira. Wani kuma yakan gane sassan rayuwa ne wadda ta shafi duniya, ya zama mahiri, ya tumbatsa wajen samar da qololuwar jin daɗinta.

Ta haka za a tabbatar da fahimta ita ce qashin bayan ilimi wadda za ta yi jagora ga samun jin daɗi ko muni, sannan a iya bambance abubuwa masu baragada ko baragurbi. Haka kuma shuɗewar kwanuka da yau da gobe a rayuwa wani ɗari ne na daraja a ilimi (Bergery, 1934 da kuma Hornby, 1974). Don haka neman ilimi dole ne domin rayuwa ta yi armashi. A ra’ayin Lepage (1964), a ƙasashe masu tasowa, ilimi mabuɗi ne ga abubuwa guda biyu ƙwarara:

(a) mabuɗi ne ga samun abinci. Ta hanyar ilimi ana iya kyautata noma da sana’o’i da fasaha da tattalin arziƙi da sauran 7 abubuwa da suka jivinci jin daɗin rayuwa.

(b) mabuɗi ne ga kyautata al’adu da haɗa kan jama’a, da samar da manufa ko al’ƙibla guda. Baya ga ilimin addini, ilimin zamani Bature ne ya kawo shi, don haka da harshen Bature ne wannan ilimi yake, duk da cewa ba duka muka taru muka iya Ingilishi ba.

Masana sun ce harshen da yaro ya tashi da shi, to ya fi tasiri a kansa wajen gina basira da hankali da wayo da kuma ƙwazonsa. Wannan yanayi ya bambanta da halin da ake ciki, domin muna neman ilimi da baƙon harshe. Haka ƙarin wahala ne domin sai mun iya harshen sosai kafin mu koyi ilimin. Duk da cewa Hausawa sun naƙalci iya ciniki da safara da tajirci, to amma zuwan Bature ya kawo wani sabon salo dangane da tattalin arziƙi.

Da yake babu ƙasar da za ta dogara da kanta kawai, to dole ne kafar hulɗa da mu’amala ta buqe musamman ma da waɗanda suka ci gaba. Sai dai kuma kash, hasken da ya kamata mu yi amfani da shi yana cikin harshen da ba namu ba. Saboda haka fahimtarmu da su sai an yi ɗamara, musamman da yake ai rashin sanin sirrin tattalin arziƙin ne irin na zamani ya sa aka wawashe dukiyar ƙasar a shekarun baya.

Gaskiyar magana ita ce, idan ba ka fahimci abu ba, babu wuya a ƙware ka a cikinsa. Wato dai idan kana mu’amala da mutum, ya fahimci ba ka naƙalci sirrin abin da kuke mu’amala a kansa ba. to babu wuya a cuce ka. Rashin sanin sirrin tattalin arziki irin na zamani yana da illa, saboda haka babu makawa sai an rungume shi duk da kasancewa cikin baƙon harshe. Kowace al’umma kan dogara da wani abu a matsayin mai wanzar da rayuwa. A al’umomin da suka waye akwai addinai da suka ƙudurce akwai ubangiji.

A nan, addinin Musulunci ya daɗe a ƙasar Hausa, sai dai mafi yawan jama’armu ba su fahimci addinin ba, saboda ba su san ƙa’idojin addinin da iliminsa ba. Hakan ya faru saboda kasancewar ilimin addinin a harshen da ba namu ba, wato harshen Larabci. Tun da dukkaninmu ba mu iya Larabci ba, to da wuya kowa da kowa ya sami sukunin karanta littattafan addini. Don haka dole ne a dogara ga ‘yan tsirarun mutanen da suka iya Larabci domin koyon addini ta kansu. Sauran maganar ita ce shin ko hakan zai wadatar?

To a gaskiya ko da a harkar addini ba a rasa marasa gaskiya, waɗanda za su yi cuta su ribatu da jahilcin mutane. Saboda haka, maslaha ita ce fassare-fassare na littattafan addini zuwa harshenmu domin fahimtar addini sosai. Masana sun yi ittifaƙi cewa al’ada ita ce tarin hanyoyin rayuwar jama’a, musamman hikimominsu da fasaharsu da wayewarsu da iliminsu da hulɗoɗinsu da mu’amalarsu da kaɗe-kaɗensu da raye-rayensu da kuma sauran irin su.

Kafin zuwan Musuluni ƙasar Hausa, adabin Hausawa na baka ne, wato waƙar baka da tatsuniyoyi da kuma labaru. Zuwan Musuluni ya sa wasu suka san Larabci har suka fitar da ajami a matsayin hanyar rubutu. Ta ɗaya haujin kuwa, zuwan Turawa ya kawo mana iya rubuta Hausa da boko.
Harshe shi ne abin furta ra’ayoyi da ma’anonin al’adu, saboda haka, dangntakar da take tsakanin harshe da al’ada ƙaƙƙarfa ce. Wato ƙarfin ya kai babu yadda za ka koyi wani harshe ko ka yi nazarinsa ba tare da ka san al’adar masu harshen da ladabin amfani da shi ba. Ga misali, saboda irin wannan ladabi na amfani da harshe, masana suke cewa koyon harshe da koyar da shi ba zai yiwu ba sai da fahimtar al’adar masu harshen. Tun da yake haka ne kuwa, to ta tabbata kenan cewa akwai dangantaka mai ƙarfi tsakanin harshe da al’ada.

Kammalawa: Daga abin da ya gabata dangane da matasayi da ƙimar harshe da al’ada, ta tabbata cewa haɓakarsu (wato harshe da al’ada), tana share fagen ci gaban al’umma mai ɗorewa. Da farko dai akwai ƙorewar tsarin zamantakewa, wato da harshe da al’ada ne ake sarrafa muhimman batutuwan da suka gina tsarin zamantakewar al’umma. Irin waɗannan batutuwa sun haɗa da harshe da addini da ilimi da auratayya da kuma yin sulhu a tsakanin al’umma.

Akwai kuma ilimi na sarrafa tadoji da aka gada tun iyaye da kakanni, da suka haɗa da ilimin noma da tsarin cimaka da kiwon lafiya da rainon yara ƙanana da kayan gine-gine da kuma amfani da sarrafa muhalli. Wannan tsari da aka gada tun iyaye da kakanni, da harshe da al’ada ne ake tafiyar da su, saboda haka duk wani tasiri ma a bisa wannan tsari yake ci gaba da tafiya. Shi tasiri yanayi ne na haɗuwa da baqin al’adu a sanadiyar hulɗa ko mu’amala tare, daga nan kuma sai kwaikwayo da aro su bijiro a sanadiyar tasiri a kan juna. Ta haujin al’adun gargajiya ma, da haɓakar harshe da al’ada ne ake sarrafa su. Wato da waxannan ne (waɗanda sun haɗa da sana’o’i na samun abin ɗawainiyar kai da kuma iyali gaba ɗaya).

A gaskiya ma, waɗannan hanyoyi na al’ada, naƙaltarsu ake yi kuma iliminsu na ƙorewa tun daga iyaye daga kakanni. Akwai kuma batun wasu al’adu na musamman, waɗanda al’umma suka ɗauka da matuƙar fa’ida da muhimmanci. Hasali ma, irin waɗannan al’adu na musamman (waɗanda kuma ake sarrafawa da harshe a cikin ma’auni na al’ada) suna taka muhimmiyar rawa a rayuwar al’umma. Ga misali, ɗauki maganganun hikima da azanci da aka san a harsunan al’umma 9 ne suke qumshe da kuma ɗimbin al’adun da suke koyarwa.

Akwai adabi (wanda ya ƙumshe zube da waƙa da kuma was an kwaikwayo) da zane-zane da raye-raye da waƙe-waƙe da labarum gargajiya da ayyukan hannu da kuma fina-finai. Bugu da ƙari gudummawar harshe da al’ada ba a baya suke ba, dangane da yaɗa ilimi, musamman ma irin wanda zai haɓaka basira da aiki da basira da hikima ta ƙirƙira da kuma dabarun gina al’umma a matsayinsu na ɗaiɗaiku da kuma a ƙungiyance. Ana kuma tace gurvatattun tadoji da al’adu, sannan a yi watsi da su domin kada su cutar da al’umma (musamman ma yara manyan gobe). Harshe a matsayinsa na hanyar furuci mai ma’ana, shi ne al’umma ke sarrafawa cikin magana domin isar da saƙon da ke zukatansu na abin da ya shafi rayuwarsu ta yau da kullum.

Kenan tasirin harshe da al’ada ga al’umma tamkar rayuwa ce da ruhinta, wato harshe ba ya wanzuwa sai idan akwai al’ummar da ke amfani da shi. Haka kuma, al’umma ba ta iya gudanar da al’amuran rayuwarta sai ta yi amfani da harshe a cikin dangantaka da al’ada. Ashe kenan ɗaya ba ya yin tasiri sai da ɗayan.

A gaba ɗaya dai harshe da al’ada haɓaka ce ta muhimman abubuwa guda biyu da suka zamo kafa wadda ɗaiɗaikun mutane (da kuma ma a ƙungiyance) suke bayyana ƙwazo da hikima da kuma karsashinsu na gina kansu (da al’umarsu). Saboda haka, harshe da al’ada suna daga cikin vangarorin ci gaban al’umma mai ƙorewa.

Farfesa Salisu Ahmad Yakasai Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato [email protected]