‘Ya’yan mu da shaye-shayen kayan maye (2)

Daga AISHA ASAS

Idan ka sama wa ‘ya’yan ka uwa tagari to ka ba su kaso sittin bisa ɗari na tarbiyya. Uwa mai ilimi ce ta san fara tarbiyyar ‘ya’ya tun daga ɗaukar cikin su ne ba bayan haihuwa ba.

Manzon (S.A.W) ya sanar da mu addu’a da ya ce ‘duk ma’aurata da su ka zo kwanciyar aure su ka karanta ta, idan an ƙadaro shigar ciki a wannan kwanciyar Allah zai nisanta ɗan da shaiɗan.

“Allahumma janibnan shaiɗan ana, wa janibnan shaiɗan ala ma razaƙana” wannan kuwa mai ilimi ce kawai ta ke yin ta, ta ke tunawa mijin ta.

A lokacin da ‘ya’yan ku su ka fara girma za ta tarbiyyantar da su bisa tafarkin da ya dace. Za ta koyar da su sanin ya kamata, ta tsoratar da su da ƙin hanyar ɓata.

Anan zan ce idan maigida ya samu hakan sai ya gode wa Allah, domin ya samu sauƙin tarbiyya ta cikin gida. Amma fa hakan ba ya na nufin ya sakar wa matar sa ragamar tarbiyyar dukan ta ba.

Bayan rashin tarbiyya akwai hanyoyi biyu da kan iya kai ‘ya’yan mu ga tafarki na shaye-shaye:

Muhalli: A nan ina magana kan unguwa. Idan ka fahimci unguwar da ka ke ko garin da ku ke ciki akwai yawaitar ma su shaye-shaye, to ka kwana da shirin yiwuwar yaran ka su koya, domin kwakwalwar yaron da ba shi da wayo sosai ta na kallon abinda ya yawaita a matsayin abin da ba shi da laifi. A nan ina so in haska haske ga iyaye akan duhun da su ka jima a cikin sa ba tare da sun sani ba. Ka na da baƙwabci, ‘ya’yan sa na abin da su ka ga dama, watakila don ba su yi dace da uwa tagari ba. Tun su na yi a ɓoye don kar baban su ya sani, kai kuwa ka na ganin su sai ka dinga kawar da kai a cewar ka bai shafe ka ba.

Idan ka dawo gida sai ka yi wa na ka ‘ya’yan kashedi kan alaƙa da yaran, kai a naka gani ka nisanta gidan ka da cutar, shi kuwa maƙwabcin ka ya je can ya ƙarata. Abin da ba ka sani ba ya kai maigida, ba makwabcin ka kawai ka cuta ba har da kan ka. Ta yaya?

Waɗannan yaran da ka ce ba ruwan ka da su za su iya zama silar gurvacewar tarbiyyar na ka ‘ya’yan, duk da cewa ka hana su hulɗa. Idan ba sa abota da na ka ‘ya’ya ai su na yi da na wasu maƙwabta, wanda su kuma ‘ya’yan ka za su iya abota da su. Ma’ana sun koyawa na wasu, sai na ka su koya gurin su.

Matsalar gurɓacewar rayuwar yara tamkar cuta ce mai yaɗuwa, wadda za ta iya baibaye duk yaran da ke kewaye da ita, musaman matsalar shaye-shaye. Ina mafita? Idan ɗan maqwabcin ka na yin ba daidai ba, ka da ka kawar da kai, yi iyakar qoqarin ka don daidaita shi ko da hakan na nufin sanar da baban sa tun abin bai yi girma ba. Idan kuwa ya nemi taimakon ka ka taimaka ma sa tamkar ɗan ka ne ke son lalacewa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *