Muhammad bin Abdulkarim al Maghili (1440 – 1505)

Daga FATUHU MUSTAPHA

An haifi Muhammad bin Abdulkarim al Maghili a alƙaryar Tabalbala dake Tilmisan na Ƙasar Magrib (Algeria) a shekarar 1440. Asalin sa ɗan ƙabilar Maghila ne daga babbar ƙabilar nan ta Berbers. Tun tasowar sa ya maida himma wurin neman ilmin addini a fannoni da dama, ya fara karatun sa a gidan su, daga baya da ya fara kaɓura sai ya shiga makarantar wani shehin malami da ake zancen sa a wannan lokaci, Imam Abdulrahman al Tha’alabi, da ya ƙara tumbatsa sai kuma ya koma karatu a ƙarƙashin wani bajimin malamin, Abu Zakariya Yahya ibn Yadir ibn ‘Atiq al-Tadalsi wanda ya rasu a shekarar 1475 bayan an masa alƙali a Tuat. Ganin karan sa ya kai tsaiko a fagen ilmin fannoni, sai ya shirya wata tafiya zuwa ƙasashen Larabawa, inda anan ne ya nazarci tsarin shari’ar Musulunci da matsayin kafiran amana wato Dhimmi.

Bayan ya dawo ne sai ya yi birki a babban birnin ƙasar Moroko wato Fez, inda anan ya fara shan daga da malamai akan matsayin Dhimmi a daular Musulunci. A farkon fara wannan muhawara, ya samu goyon bayan sarkin Fez na wannan lokaci, Sultan Abu Zakariyya al Wattasi, to amma ba a jima ba wannan rikici ya nemi ya janyo wata mummunar gaba tsakanin sarkin da manyan malaman lasar, hakan ta sanya sarkin ya kore shi daga ƙasar Maroko.

Bayan ya bar Fez sai ya sauka a garin Tamantit da ke yankin Tuat, wannan gari shi ne ke kan iyakar lasashen Sudan da na Larabawa, kuma gari ne na kasuwanci da harkokin arziki. A wannan gari sai ya lura cewa mafiya akasarin masu kuɗin garin Yahudawa ne, hakan kuwa ta faru ne saboda yadda suka yi amfani da dammar su ta hanyar yin sana’o’in da musulmi ba su iyawa. Ganin haka sai ya maida himma wurin nuna ilolar zama da Yahudawa, ya kuma yi sa’a talakawan musulmi suka bas hi haɗin kai, ya kuma samu taimakon babban ɗan sa Abduljabbar. Cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ya wa’azin sa ya haifar da rikicin da ya sanya musulmi suka farwa Yahudawa, sukia fatattake su daga garin.

Ganin wannan ƙura da ya tayar, da har ma ya sanya farashin misƙal 7 ga duk wanda ya Kashe Bayahude ya kawo masa kan sa, ya tattara ya nasa ya nasa ya bar garin. Wannan ra’ayi nasa a wannan lokaci ya qara samun tagomashi ne, sakamakon rikicin ƙasar Andalus, inda Sarauniya Isabella ta yi nasarar ruguza gwamnatin musulunci a ƙasar, ta kuma kori dukkan wani musulmi da ya ke ƙasar, inda da daman su suka gudo Maroko. Ganin irin halin da musulmin ƙasar Andalus (Spain) suke ci, ya sanya musulmi da yawa sun amsa kiran na sa, na ayaƙi Yahudu da Nasara da ke zaune a ƙasashen musulmi. A haka har ya sanya wasu matasa suka rusa tare da ƙone wani babban wurin bautar Yahudawa suka kashe musu manyan malamai a Tuat.

Wannan rikici da ya faru sakamakon saƙlon wa’azin sa, shi ne ya sanya ya tattara kayan sa ya kama hanya zuwa ƙasashen Sudan ta Tsakiya (Afirka ta Yamma), inda ya fara sauka a fadar Sarkin Agades, Abdullahi Sotofon. Wannan ziyara kuwa ta zo masa da buɗi, domin kuwa ya samu kyakkyawar tarba a fadar. Inda daga nan ne ya samu dammar ziyartar manyan masarautun dake wannan yanki, ciki kuwa har da Takedda, Katsina, Kano da kuma tsohon birnin nan mai tarihi, Gao wanda shi ne Babban Birnin Daular Songhai.

Daga nan ne ya shigo Kano a zamanin sarkin Kano Muhammadu Rumfa, wannan ziyara ta buɗe wani sabon shafi a tarihin Kano, domin kuwa ya zo a daidai lokacin da wani bajimin malamin ya zo shi ma wanda ake kira Abdulrahman Zaghaiti. Sheikh Abdulrahman ya iso Kano kwana uku kafin zuwa Almaghili, kuma kamar yadda Aslil Wangariyun ta yi bayani, sarki ya yi maraba da zuwan waɗannan malamai. A lokacin wannan ziyara ne ya kawo sauye sauye a yadda ake tafiyar da shugabanci a ƙasar Kano da Katsina.

A wannan lokaci ya rubuta littafin nan mai suna Taj al Din fi ma Yajub alal mulk. Wannan littafi ya rubuta shi ne, akan tsarin shugabanci a musulunci, sakamakon roƙon da Sarkin Kano rumfa ya yi masa akan ya rubuta masa littafi da zai zamar masa jagora wurin tafiyar da al’amurran siyasa da mulkin ƙasar Kano. A wannan lokaci ne kuma ya rubuta wani littafin mai suna Jumla al Mukhtasara, wato takaitaccen bayani akan yadda za a magance matsalar tsaro da hukunta ma su laifi.

Daga Kano ne ya koma Katsina a zamanin Sarkin Katsina Muhammadu Korau. Zuwan sa Katsina ne, ya haɗu da wani almajirin sa, Shamsuddeen al Anusammani al Taƙiddawi (wani baƙar fata mutumin Takedda). A wannan zuwan ne kuma ya haɗu da shehin malamin nan da ya taɓa zama a Kano, kafin ya koma Katsina Sheikh Umar al Aƙit, wanda aka fi sani da Wali Ɗantakuma, shi ne daga baya aka naɗa shi ya zama alkalin Katsina. Zaman sa a Katsina ya ƙara samun tagomashi musamman ganin yadda ya kafa ya kuma raya jami’ar nan mai tarihi ta Gobarau, wadda it ace ta samar da manyan malamai irin su, Wali Ɗanmarina da Wali Ɗanmasani.

Daga Katsina ne ya tafi ya zuwa Gao dake daular Songhai, ya sauka a Gao a zamanin Sarkin Songhai Askiya Muhammad Turi. Ya sauka ne jim kaɗan bayan Muhammadu Turi ya wargaza tsohuwar Daular Sonni wanda ya zarga da hargitsa addinin musulunci da kuma ɓata shari’a. a wannan ziyara tasa ne, Muhammadu turi ya gabatar masa da tambayoyin da ya nemi ya ba shi amsa, akan matsayin juyin mulki a Musulunci, haraji, bayi da sauran su. A kuma wannan lokaci ne ya baiwar sarki shawarar da ya hallaka dukkan malaman Mausufa masu goyon bayan rusasshiyar gwamnatin Sonni.

A wata faɗar an ce yana nan ne ya samu labarin cewa Yahudawa sun Kashe ɗan sa Abduljabbar, amma wasu sun ce bayan ya dawo Kano ne, wasu kuma sun ce ya samu labarin ne bayan ya koma Katsina. Ya dai roƙi Askiya Turi da ya bashi sojoji da zai je ya yaƙi Yahudawa a Tuat, amma wannan roƙo na sa baio samu nasara ba. Ya kuma baiwa Askiya Turi shawarar da ya yaƙi dukkan Yahudawan da suke ƙasar sa, wannan shawara ta janyo rikici tsakanin sa da Alƙalin Songhai Mahmud bin Umar. A saboda haka Askiya Turi ya sallame shi ya komo Katsina.

Daga ya komo Kano, inda ya cigaba da zama a gidan sa da ke Zauren Tudu ya kuma yi aure ya haifi ɗa da ya kira da Sidi Baƙi. Kamar yadda na bayyana a baya, ance a wannan lokaci ne ya samu labarin cewa Yahudawa sun kashe ɗan sa. Dan haka ya ɗauri aniyar ya koma domin ya ɗauki fansa. Sai ya rubuta wasiƙa ya aikawa Askiya Muhammadu Turi da ya taimaka masa da dakarun da zai je ya yaƙi Yahudawa, wanda a wannan lokaci ma dai wannan buƙata ta sa bata samu shiga ba.

Ganin haka sai ya tarkata iya dakarun da ya samu daga Kano da Katsina da Agades ya nufi Tuat. Inda ya fara yi musu kwanton vauna a Tamentit sannan ya kuma kai musu hari a Tuat. Wannan nasara da ya yi ta ba shi damar yi musu hawan ƙawara, inda ya tursasu da cewa kodai su karɓi addini, ko kuma su zauna cikin wulaƙanci. Bayan wannan ne ya kafa zawiyyar sa a Bu Ali a Tuat kuma anan ne Allah ya yi masa rasuwa a shekarar 1505. An dai yi zargin cewa Yahudawa ne suka shirya masa guba a abinci ya ci, wasu kuma sun ce ya rasu ne bayan ya sha fama da rashin lafiya.