Yadda za a kula da tsaftar haƙora

Daga AISHA ASAS

Haƙora na ɗaya daga cikin ɓangarorin jiki da su ke bayyanar da tsafta ko ƙazantar mai su. Da yawa mu na ƙorafin bakin mu na wari ba dalili, alhali rashin kulawa da haƙori ya janyo hakan. Duk da cewa akwai matsalolin da ka iya haifar da warin baki ko da kuwa ana matuƙar kula da shi, kamar ciwon olsa da sauran su. Duk da haka kula da baki yadda ya kamata makami ne babba na yaƙar warin baki.

Uwargida ki sani, saka makilin a magogi (burushi) ki goge baki da safe ba shi kaɗai bakin ki ke buƙata ba, asali ma akwai wanda ya fi shi muhimmanci. Da yawan mu ba mu ɗauki wanke baki kafin kwanciya wani abu mai muhimmanci ba, bayan kuwa ya na daga cikin manya-manyan hanyoyin tsaftace haƙora.

Uwargida ki misalta da tunanin ki, kin ci abincin dare watakila har da nama a ciki, yayin da ki ke cin watakila wani ya yi nasarar samun wani saƙo ya ɓoye. Ba ki wanke bakin yadda ya kamata ba, kin sha ruwa kin kwanta. Bakin a rufe tsayin wasu awanni, ba iskar da ke yawo a ciki, sannan ba motsin da zai fitar da abincin har ki tofar da shi. me ki ke tunanin zai zama makomar wannan guntun abincin? Zai ruɓe a bakin, ya zama wata ƙwayar cuta da za ta iya cutar da haƙora, ko ta sanya warin baki.

Ya zan kula da haƙora na?

Uwargida za ta guji cin albasa ko tafarnuwa a lokacin da za ta kwanta barci. Idan har ta ci to ta daure ta samu aƙalla awanni uku kafin ta yi barci. Ta kuma tabbatar ta na abin da zai dinga buɗe bakin akai-akai iska na shiga ciki don warin ya fita.

Uwargida ta sa wa ranta wanke bakin ta a duk bayan cin abinci, ba dole sai da makilin ba, za ta kuskure bakin sosai da ruwa da ɗan yatsa.

Uwargida ta mayar da shi wajibi wanke baki da buroshi ko asuwaki a kowace safiya da kuma da dare lokacin barci.
Uwargida idan da hali ki yawaita asuwaki domin ya na kawar da warin baki, ya ƙara wa haƙora ƙarfi tare sanya su haske.

Uwargida ta koyi yadda ake wanke baki da buroshi ko wanin sa, ba wai yadda mu ke yi ba, mu ɗora buroshi kan haƙora mu darje ba tare da damuwa da shigar sa tsakanin haƙora ba, kuma ki tabbatar ki na goge harshe cikin tausasawa.

Uwargida ki sani, ganyen Na’a-na’a ganye ne da ke gyara baki, ya na kashe ƙwayoyin cuta da ka iya haifar da tsutsar haƙora , zai kuma hana baki wari.

Uwargida ta riqe kanumfari sosai don gyaran haƙoran ta. Da safe ki jefa biyu ko uku a baki, ki na taunawa a hankali har ya zama gari. Zai shiga cikin haƙoran ki da taimakon yawun bakin ki, kuma zai mamaye baki wanda zai kashe ƙwayoyin cuta.

Uwargida za ta samu ciyawar ‘Sana maki’ ta haɗa ta da ganyen Na’a-na’a da ɗan gishiri kaɗan. A nan ki na da zaɓi biyu; ko dai ki dinga ɗiban kowane daga cikin su ki sa a baki, sai kin haɗa su sai ki dinga taunawa har ya watse ba tare da kin haɗiye ruwan ba, ki bar shi a baki tsayin ‘yan mintuna. Ko kuma ki haɗe su guri ɗaya a dake sai ki yi amfani da magogi ki na goge ko’ina na bakin.

Daga ƙarshe mu sani, tsaftar baki wajibi ce matuƙar ba ma son mutane su kyamace mu. Duk kwalliyar ki Hajiya idan aka ji bakin ki na wari za a rena ki tare da kyamar kusanto ki.