Tawagar PDP ta ziyarci Gwamna Bello

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Neja Abubakar Sani Bello, ya karɓi baƙuncin tawagar kwamitin sulhu na jam’iyyar PDP a yammacin Alhamis.

Tawagar ta ƙunshi Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki, da Tsohon Gwamnan Neja, Dr Mu’azu Babangida Aliyu, da Tsohon Gwamnan Gombe, Ibrahin Hassan Dankwambo, da Tsohon Gwamnan Katsina, Ibrahim Shema da fai sauransu.

Tawagar ta ziyarci Gwamna Bello ne domin jajanta masa game da sace ɗaliban sakandare da ‘yan bindiga suka yi kwanan nan.

Gwamna Bello ya wallafa bayanin ziyarar a shafinsa na twita a yammacin Alhamis.