IMO: An buƙaci Buhari da shugabannin APC su shiga tsakanin Uzodima da Okorocha

Daga AISHA ASAS

Wani gungun magoya bayan dimukraɗiyya sun gudanar da zanga-zangar lumana a Abuja inda suka nuna rashin jin daɗinsu dangane da kama tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okoroca, da ‘yan sanda suka yi tare da yin kira ga Shugaba Buhari da sauran shugabannin APC a kan su gaggauta shiga tsakani.

An ga masu zanga-zangar ɗauke da kwalaye waɗanda aka rubuta saƙonni daban-daban a jikinsu masu nuna rashin kyautatuwar abin da Gwamnan Imo, Hope Uzodima ya yi da kuma nuna goyon baya ga Rochas.

Masu zanga-zangar sun ra’ayin cewa kama Okorocha da aka yi take-take ne na neman hana shiyyar Kudu maso-gabas samun kujerar shugabancin ƙasa ya zuwa 2023.

Gungun masu zanga-zangar wanda haɗaka ce ta ƙungiyoyin matasa daban-daban, sun ce ba zai yiwu a tilasta wa jam’iyyar APC don ta bauɗe daga tsarin miƙa damar shugabanci ga yankin Kudu maso-gabas a 2023 ba.

A cewarsu, “Okorocha ya sauke nauyin da ya rataya a kansa a jam’iyyarmu. Shi kaɗai ya yi tsayin daka wajen ɗaukaka APC a Kudu maso-gabas a wancan lokaci yayin da shi kuma gwamna mai ci yana PDP yana yaƙar sa saboda kawo APC shiyyar Kudu maso-gabas. Ya samu cigaba inda ya zama Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin APC kuma ya yi ma ƙungiyar aiki bilhaƙƙi, abu ne mai wahalar gaske a iya auna son da yake yi wa APC……”

Haka dai suka zayyana kyawawan abubuwan da suka yi iƙirarin Okorocha ɗin ya yi don amfanin ƙasa da ma shiyyarsu ta Kudu maso-gabas.

A bisa wannan dalili ne matasan suka nuna akwai buƙatar Gwamna Hope Uzodima ya koyi ɗora aiki daga nasarorin da ya tarar magabacinsa ya samu don amfanin al’umma.

An sa ‘yan sanda su kama Okorocha ne a Lahadin da ta gabata bisa zargin shiga harabar rukunin gidajen Royal Spring Palm wanda aka danganta da matar Okorocha, Nkechi, bayan da hukuma ta haramta shiga rukunin gidajen don ba ta damar gudanar da bincike.

A wata hira da Okorocha ya yi da manema labarai a lokacin da ya karɓi baƙuncin magoya bayansa a Owerri, a ranar Litinin, Okorocha ya ce bai taɓa kama kowa ba a lokacin da yake gwamnan Imo.