Yadda na sayar da kadarorina don bada tallafin karatu ga ɗaliban Kano 370 – Kwankwaso

Daga AISHA ASAS

Gwamnan Jihar Kano na dauri, Rabiu Kwankwaso, ya bayyana yadda ya sayar da wasu kadarorinsa domin ɗaukar nauyin ɗalibai ‘yan asalin Kano su 370 zuwa karatu a ƙasashen ƙetare a ƙarƙarshin Gidauniyar Kwankwasiyya.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a lokacin da ya je tarbar ɗaliban da suka ci gajiyar shirin da suka dawo daga Indiya da Dubai a babban filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda ya bayyana gamsuwarsa dangane da ayyukan gidauniyar.

Tsohon Ministan Tsaron ya ce a lokacin da ya yanke shawara kan batun ɗaukar nauyin ɗaliban sai ya ji ya gamsu da ya ɗebi dukiyarsa ya cika kuɗirinsa wanda hakan ya sa ala tilas ya sayar da wasu kadarorinsa.

Ya ce ɗalibai 370 da suka ci gajiyar shirin an tura su karatu ƙasashen Indiya da Dubai ne haɗa da ɗauke musu kuɗin jirgi da na masauki.

A cewar Kwankwaso, “Sha’wata ga ilimi abu ne da ba shi da iyaka. Sai da ya kai ga na sayar da kadarorina domin tabbatar da shirin bada tallafin karatun ya kankama ƙarƙashin Gidauniyar Kwankwasiyya.”

Daga nan ya nuna farin cikinsa ganin ɗaliban sun dawo gida lafiya.

A ɓangare guda, jagoran ɗaliban, Yusuf Dala, ya yaba wa Kwankwaso a madadin ‘yan’uwansa dangane da hidimar da yi na tallafa musu zuwa karatu a ƙetare.

A Satumban 2019 ne ɗaliban suka bar Nijeriya zuwa ƙasashen waje don zurfafa karatu a bisa ɗaukar nauyin Kwankwasiyya Development Foundation.