Nijeriya: An samu ƙaruwar matsalolin tsaro a ‘yan makonnin da suka gabata – Abdulsalami

Daga FATUHU MUSTAPHA

Tsohon Shugaban Ƙasa kuma Shugaban Kwamitin Zaman Lafiyar Ƙasa (NPC), General Abdulsalami Abubakar, ya ce a tsakanin makonni biyun da suka gabata matsalar rashin tsaro da rashin haɗin kai sun ƙaru a sassan Nijeriya.

Don haka ya yi kira ga gwamnoni da su gyara ɗarama sannan su maganace waɗannan matsaloli da ke faruwa a jihohinsu.

Abdulsalam ya yi kira ga ‘yan ƙasa da a kasance masu haƙuri da juriyar mawuyacin halin da aka shiga, sannan a zamo masu sadaukarwa wajen daidaita lamurran ƙasa.

Tsohon Shugaban Ƙasar ya yi wannan gargaɗi ne yayin ganawar da ya yi da manema labarai a Talatar da ta gabata a Minna, babban birnin Jihar Neja.

Ya ce ganin yadda ake zaman ɗar-ɗar sakamakon rikice-rikicen ƙabilanci a wasu sassan ƙasa ya sanya kwamitinsa sa baki wajen kira ga ‘yan Nijeriya da a yi haƙuri a zauna da juna lafiya a irin wannan mawuyacin lokaci.

A cewarsa, “A irin wannan lokaci akwai buƙatar bakiɗaya mu haɗa hannu wajen magance matsalolinmu don tabbatar da haɗin kan ƙasa. Bai kamata mu ɓata lokaci wajen ɗora zargi a kan juna ba.

Yayin da ya yaba da ƙokarin Shugaba Muhammadu Buhari wajen ƙoƙarin samar da daidaito, Abdulsalam ya yi kira ga gwamnoni da su miƙe tare da ɗaukar matakan tabbatar da lumana a jihohinsu.