Kotun Ƙoli ta yi fatali da ƙarar PDP kan nasarar Gwamnan Benuwe 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kotun Koli ta yi fatali da karar da aka daukaka kan zaben gwamna Hycinth Alia na jihar Benuwai.

Matakin na zuwa ne bayan janye karar da lauyan Mr Titus Uba na Jam’iyyar PDP, Sebastian Hon ya yi.

Titus Uba ya kalubalanci nasarar gwamna Hyacinth ne na jam’iyyar APC.

Sai dai kotun kararrakin zabe da ta daukaka kara a Abuja sun tabbatar Alia ne halastaccen gwamnan jihar ta Benue bayan da hukumar zabe INEC ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaben ranar 18 ga watan Maris.

Kotun daukaka karar ta ce ba ta da hurumin sauraron karar da aka shigar gabanta saboda batutuwan da aka yi korafi a kansu sun faru ne gabanin zaben.

Kotun ta kuma ce kamata ya yi Uba ya maka mataimakin gwamna Sam Ode a babbar kotu bisa zargin mallakar takardar boge.

Ta kuma ce Uba ya gaza tabbatar da zarge-zargen da yake yi wa mataimakin gwamnan.